For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Shari’ar Atiku, Ta Yi Kira Ga Tinubu Da Ya Rage Yawan Ministoci

Gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyyar PDP tare da jagororin jam’iyyar da suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar sun haɗu a Abuja domin tattauna makomar jam’iyyar.

A wajen zaman tattaunawar da jagororin PDPn suka yi, sun jaddada alƙawuransu na ci gaba da yi wa jam’iyyar biyayya domin samun ci gabanta.

Da yake karanta jawabin bayan taron, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce, taron ya mayar da hankali kan buƙatar samun tarbiyya a jam’iyyar tare da nuna ƙin jinin duk wani yunƙuri na cin amanar jam’iyya da yi mata zagon ƙasa.

Ya ce babu wani mutum guda ɗaya ko wani gungun mutane da za a bari ya wargaza haɗin kan ƴan jam’iyya da tsare-tsarenta.

Bala Mohammed ya ce, taron kuma ya mayar da hankali wajen sake fasali da kuma ƙarfafa jam’iyyar, wanda a dalilin haka ya sanar da cewa, an ci gaba da samar da sasanto da waraka a kan matsaloli da saɓani sannan kuma ana samun nasara.

Ya ce, taron ya amince da cewar haɗin kai da miƙa wuya ga jam’iyya sune jigon jam’iyyar PDP, kuma duk masu tabbatar da hakan za a saka musu da alheri.

Gwamna Bala Mohammed ya kuma ce, dukkan gwamnonin PDP, da shugabanninta a ɓangarori daban-daban na goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar da ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Ifeanyi Okowa wajen ganin sun ƙwato nasarar da aka sace musu, sannan zasu yi duk mai yiwuwa wanda ya dace da shari’a wajen ganin nasarar hakan.

Ya ƙara da cewa, gwamnonin jam’iyyar zasu yi aiki tare da jam’iyya a matakin jihohi domin tabbatar da an sami kyakkyawan jagoranci, gaskiya da riƙon amana.

Jagororin PDPn sun kuma kushe yawan adadin ministocin da Bola Ahmed Tinubu ya miƙawa Majalissar Dattawa domin tantancewa.

Sun ce, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta nuna iya jagoranci wajen rage kuɗaɗen da ake kashewa a gudanar da gwamnati, inda suka ce ya kamata a rage yawan ministoci daga 48 da kuma tarin masu bayar da shawara da mataimakan da ake shirin naɗawa domin samar da lafiya ga arziƙin ƙasa.

Haka kuma taron ya yi kira ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya guji shiga yaƙi da ƙasar Nijar a kowanne yanayi kan juyin mulkin da aka yi a ƙasar, sai dai ya yi amfani da hanyoyin tattaunawa da diflomasiyya wajen magance matsalar.

Waɗanda suka sami halartar taron sun haɗa da Atiku Abubakar, Ifeanyi Okowa, Gwamna Bala Mohammed (Bauchi), Gwamna Ahmadu Fintiri (Adamawa), Gwamna Duoye Diri (Bayelsa), Gwamna Sheriff Oborevwori (Delta), Gwamna Peter Mbah (Enugu) da Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun.

Sauran sun haɗa da Gwamna Godwin Obaseki (Edo), Gwamna Kefas Agbu (Taraba), da kuma Gwamna Dauda Lawal Dare na Jihar Zamfara.

Haka kuma Shugaban Riƙon Jam’iyyar PDPn, Umar Damagum, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Shiyyar Kudu, Taofeek Arapaja, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kudu maso Kudu, Dan Orbih da wasu da dama sun halarci taron.

Comments
Loading...