A harin da ƙungiyar ISWAP tai iƙirarin kai wa gidan yarin Kuje da ke Abuja ranar Talatar da ta gabata wanda yai sanadiyyar kuɓutar da manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram 64, rayuwar wasu manyan Najeriya da ke zaman waƙafi a gidan yarin ta shiga ruɗani.
Rahotanni sun nuna cewa, an kitsa tare da kai harin ne domin kuɓutar da ƴan ta’addar waɗanda wasun su suka ɗebe shekaru goma a cikin gidan yarin suna jiran hukunci.
Cikin manyan da ake tsare da su a gidan yarin Kuje a yayin da aka kai harin akwai, dakataccen mataimakin kwamishinan ƴansanda, Abba Kyari, tsohon Gwamnan Jihar Plateau, Joshua Dariye da takwaransa tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Jolly Nyame, waɗanda duk su biyun Shugaba Buhari ya yi musu afuwa.
Akwai kuma tsohon shugaban hukumar fansho ta ƙasa da aka kama da laifi, Abdulrasheed Maina da kuma tsohon ɗan Majalissar Wakilai, Farouk Lawan duk a gidan yarin na Kuje.
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Ƙasa, Abubakar Umar, ya ce, gidan yarin na da ƙarfin ɗaukar mutane 940 ne, amma a lokacin da ƴan ta’addar suka kai harin akwai fursunoni 994 a cikinsa.
Ya ƙara da cewa, fursunoni 443 da suka tsere an samu nasarar dawo da su abinda ya sa yanzu haka akwai fursunoni 578 a gidan yarin.
Cikin waɗanda suka tsira, Umar ya ce, akwai ƴan Boko Haram guda 64 abun da yasa adadin waɗanda suka tsere ya kai 416.
Akwai kuma rahotannin da ke nuni da cewa, fursunoni 4 sun rasa rayukansu a yayin harin.