For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Manyan ‘Yan Siyasa 22 Da Suka Debe Shekaru 22 A Gwamnati

A wani bincike da jaridar DailyTrust ta gabatar, ta gano ‘yan siyasa 22 da suka kasance ana damawa da su tun farkon lokacin da mulkin demokaradiya ya dawo Najeriya a shekarar 1999.

Wadannan ‘yan siyasa sun kasance a gwamnati ne ta hanyar tsallakawa daga wannan mukami zuwa wancan mukami.

Wadansun su sun fara tun daga shugabancin karamar hukumarsu, wasu daga nade-nade, wasu daga gwamna, wasu ‘yan majalissu da dai sauransu.

Ga jerin sunayen da jaridar ta DailyTrust ta fitar:

  1. Ahmad Lawan

Shugaban Majalissar Dattawa ta yanzu, kuma mutum na 3 a girman mukami a Najeriya, ya fara a matsayin dan Majalissar Wakilai ta Tarayya tun 1999.

Ya debe shekaru 8 a majalissar yana wakiltar mazabar Majalissar Wakilai ta Bade/Jakusko kafin daga baya ya koma Majalissar Dattawa a shekarar 2007 inda ya ke wakiltar mazabar Yobe ta Arewa a Majalissar Dattawan.

  • Danjuma Goje

Sanata ne mai ci a yanzu, yana wakiltar mazabar Gombe ta Tsakiya a Majalissar Dattawa ta Najeriya.

Da farko a shekarar 1999 ya fara a matsayin karamin Ministan Lantarki karkashin gwamnatin Obasanjo, daga baya kuma a shekarar 2003 ya zama Gwamnan Gombe inda ya debe shekaru 8 a kan wannan kujera.

A shekarar 2011 ya zama dan Majalissar Dattawa ta Najeriya, kuma har kawo yanzu yana majalissar.

  • Ike Ekweremadu

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa kuma mafi dadewa a wannan kujera a tarihin Najeriya.

Ya fara siyasa a matsayin shugaban karamar hukumar Aninri ta jihar Enugu, daga baya a shekarar 1999 ya zama shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar Enugu zuwa 2001 wanda daga baya aka mai da shi sakataren gwamnatin jihar ta Enugu.

A 2003 ya zama dan Majalissar Dattawa mai wakiltar mazabar Enugu ta Yamma, inda a shekarar 2007 ya zama mataimakin shugaban Majalissar Dattawa har zuwa 2019.

  • Raji Fashola

Ministan Aiyuka da Gidaje a yanzu wanda ya fara a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Legas a 1999 karkashin gwamnatin Tinubu har zuwa 2007.

 Ya zama gwamnan Legas daga 2007 har zuwa 2015, wanda bayan gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar gwamnatin APC a 2015, ya zama Minista mai kula da ma’aikatu 3 da aka dunkule wanda daga baya aka raba gida 2.

A yanzu dai shine Ministan Aiyuka da Gidaje kuma yana kan kujerar ministan tun 2015.

  • Adamu Alero

Dan Majalissar Dattawa mai ci a yanzu wanda ya fara a matsayin gwamnan jihar Kebbi a shekarar 1999 zuwa 2007.

An zabe shi Sanata a 2007, inda daga baya tsohon shugaban kasa Umaru ‘Yar’adua ya nada shi Ministan Abuja.

A shekarar 2011 ya koma Majalissar Dattawa inda yake wakiltar matsabar Kebbi ta Tsakiya.

  • Aliyu Wamakko

Dan Majlissar Dattawa mai wakiltar Sokoto ta Arewa wanda ya fara a matsayin mataimakin gwamna Bafarawa a 1999 zuwa 2007.

Ya zama gwamnan Sokoto a 2007 zuwa 2015 wanda daga baya aka zabe shi a matsayin dan Majalissar Dattawa, kuma har yanzu yana ciki.

  • Rauf Aregbesola

Y afara ne a matsayin kwamishina a jihar Legas lokacin Tinubu, daga baya ya koma jihar sa ta Osun ya zama gwamna wanda ya kare a 2018.

Shugaba Buhari ya nada shi a matsayin Ministan Harkokin Cikin Gida kuma har yanzu yana kai.

  • Chris Ngige

Ministan Kwadago mai ci a yanzu, ya fara a matsayin mataimakin sakataren PDP na kasa a yankin Kudu maso Gabas kuma sakatare a yankin.

Ya zama gwamnan jihar Anambara a 2003 wanda daga baya aka cireshi saboda wasu dalilai.

A shekarar 2011 ya zama dan Majalissar Dattawa mai wakiltar Anambara ta Tsakiya har zuwa 2015.

Shugaba Buhari ya nada shi Ministan Kwadago daga 2015 zuwa wannan lokaci.

  • George Akume

Tsohon gwamnan Benue tsakanin 1999 zuwa 2007, daga baya ya zama dan Majalissar Dattawa mai wakiltar Benue ta Arewa maso Yamma na tsawon shekara 12.

A shekarar 2019, Shugaba Buhari ya nada shi Minista kawo wannan lokaci.

  1. Rotimi Amaechi

Ya fara a matsayin shugaban majalissar wakilai ta jihar Rivers tsakanin 1999 da 2007 wanda daga baya ya zama gwamnan jihar tsakanin 2007 zuwa 2015.

Shine Daraktan yakin neman zaben Shugaba Buhari wanda ya kai ga nasara a 2015, bayan nasarar shugaban ya nada shi minsta kuma har kawo yanzu shi minista ne.

  1. Orji Uzor Kalu

Ya zama gwamnan jihar Abia tsakanin 1999 zuwa 2007. Yanzu haka yana Majalissar Dattawa kuma yana cikin manyan ‘yan APC a Kudu maso Gabas da ke neman shugabncin kasa.

  1. Enyinnaya Abaribe

Ya yi mataimakin gwamna a jihar Abia tsakanin 1999 zuwa 2007 daga baya a 2007 aka zabe shi dan Majalissar Dattawa kuma har yanzu yana majalissar.

  1. Gabriel Suswam

Ya yi dan Majalissar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Katsina-Ala/Ukum/Logo daga 1999 zuwa 2007 wanda daga baya ya zama gwamnan jihar Benue tsakanin 2007 zuwa 2015.

Yanzu haka dan Majalissar Dattawa nme mai ci.

  1. James Manager

Ya zama shugaban jam’iyyar PDP na jihar Delta tsakanin 1998 zuwa 1999. Daga nan ya zama dan Majalissar Dattawa tun shekarar 2003 har kawo yanzu.

  1. Sam Egwu

Ya zama gwamnan jihar Ebonyi a shekarar 1999 daga baya ya zama minista a gwamnatin ‘Yar’adua a shekarar 2008. Yanzu haka yana majalissar Dattawa.

  1. Rochas Okorocha

Ya yi kwamishina na ma’aikatar rabon mukamai ta kasa. Ya yi gwamnan jihar Imo na shekaru 8. Yanzu haka dan Majalissar Dattawa ne kuma yana cikin wadanda ake ganin yana neman shugabancin kasa.

  1. Abdullahi Adamu

Ana masa kallon jagoran siyasar jihar Nasarawa. Ya yi gwamna a jihar tsakanin 1999 zuwa 2007. Haka kuma tun sheakar 2011 yana cikin Majalissar Dattawa.

  1. Ibikunle Amosun

A watan Afirilu na shekarar 2003 ya zama dan Majalissar Dattawa mai wakiltar Ogun ta Tsakiya. Sannan ya yi gwamnan jihar Ogun wa’adi 2.

In April 2003, Amosun was elected to the senatorial seat of Ogun Central. He was a two-term governor of Ogun State.

  1. Ibrahim Geidam

Ya kai mukamin babban sakatare a jihar Yobe, kafin daga bisani ya zama mataimakin gwamnan jihar a sheakar 2007. Yaz ama gwamnan jihar a watan Janairu na 2009 bayan rasuwar Mamman Ali. Ya kuma cigaba da kasancewa gwamna har shekarar 2019. A yanzu haka dan Majalissar Dattawa ne.

  • Abdullahi Umar Ganduje

Ya fara da mataimakin gwamna a shekarar 1999 zuwa 2003. Ya zama mai baiwa Kwankwaso shawara kan harkokin siyasa lokacin da Kwankwason yana Ministan Tsaro.

Tsakanin 2011 zuwa 2015 ya kara yiwa Kwankwason mataimakin gwamna inda a 2015 din ya zama gwamna kawo yanzu.

  • Pauline Tallen

Ta yi minister zamanin Obasanjo, sannan ta yi mataimakiyar gwamna a jihar Plateau. Yanzu haka ma minista ce a wannan gwamnatin.

  • Ali Modu Sheriff

Dan Majalissar Dattawa tsakanin 1999 zuwa 2003 sannan ya zama gwamnan jihar Borno tsakanin 2003 zuwa 2011. Ya shugabancin jam’iyyar PDP yanzu kuma yana neman shugabancin jam’iyyar APC.

Comments
Loading...