For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Masallata 8 Ne Suka Rasu, 25 Suka Sami Raunuka A Dalilin Rushewar Babban Masallacin Zaria

A ƙalla masallata takwas ne suka rasu, yayinda 25 suka ssamu raunuka a dalilin rugujewar wani sashi na Babban Masallacin Zaria mai shekaru 150 da ginawa.

Wannan ibtila’i dai ya faru ne a jiya Juma’a lokacin sallar La’asar a garin na Zaria da ke Jihar Kaduna.

Hatsarin ya faru ne da daidai misalin ƙarfe 4 na yamma, lokacin ana tsaka da sallar ta La’asar.

Ɗaya daga waɗanda suka tsira a hatsarin, Malam Shehu Nagari ya ce, lamarin ya faru a daidai lokacin da suke cikin sujjada ta biyu a sallar.

Ya ce ɓangaren masallacin da ya ruguzo ɗin, ya ruguzo kai tsaye zuwa kan waɗanda suke setin wajen suna sallar.

KARANTA WANNAN: Ɗan Majalissar Jiha Ya Samar Da Wutar Sola A Babban  Masallacin Birnin Kudu

Malam Shehu ya ce, abun da ya gani shine, ginin ya rufe waɗanda suke wajen da bulullukan ƙasa, saboda masallacin an gina shi ne da ƙasa shekaru 150 da suka wuce.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Nuhu Bamalli ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Ya ce, sun gano tsaguwa a katangar masallacin a ranar Alhamis, sannan suna shirin tura injiniyoyi zuwa wajen lokacin da hatsarin ya faru.

Sarkin ya kuma bayar da umarnin cewa, masallata su ci gaba da yin sallah a wajen masallacin har zuwa lokacin da za a kammala gyara.

Rundunar ƴansandan Jihar Kaduna ta tabbatar da cewar, mutane takwas ne suka rasu a lokacin da hatsarin ya faru.

Mai Magana da Yawun Ƴansandan, Mohammed Jalige ya ƙara da cewar, wasu mutane 25 kuma sun samu raunuka a dalilin hatsarin, waɗanda a yanzu haka suke ci gaba da karɓar magani.

Comments
Loading...