Daga: Saifuddin Madachi
An gudanar da bikin karrama tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Immigration, Muhammad Babandede, a fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje dake jihar Jigawa.
Muhammad Babandede ya kwashe shekaru 30 yana aiki da hukumar ta shige da fice, inda ya kara da shekaru 5 a matsayin mai jagorantar hukumar.
Daga bisani kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dada masa shekara daya da wata hudu.
Babandede shine shugaban hukumar na farko da ya dade akan wannan mukami, haka kuma ya samar da cigaba da sauye sauye masu tarin yawa a hukumar da suka hada da karin girman ma’aikata akan lokaci, samar da gidajen kwanan ma’aikata musamman ma a kasashen waje.
Sauran sune samar da ingantatciyar biza, inganta fasfo da dora shi ana’ura mai kwakwalwa, wanda yanzu haka Najeriya tana daya daga cikin kasashe goma masu ingantatcen fasfo a duniya.
Da yake bayyana jindadinsa game da irin tarbar da al,ummar masarautar Hadejia suka yimasa, Babandede ya nuna farin cikinsa da mamaki kan yadda yaga dandazon mutanen da suka taryeshi har zuwa Fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia, domin karrama shi bisa aiyukan da ya yi.
An shirya bikin ne karkashi jagorancin Mai Martaba Sarkin da wasu kungiyoyi.
Da yake nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Hadejia, kuma shugaban majalissar sarakunan jihar Jigawa Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje (CON), ya bayyana Babandede a matsayin da na gari wanda masarautar Hadejia, Jigawa, da kasa baki daya take alfahari da shi, in da yayi kira ga matasa masu ta sowa da suyi koyi da halayensa dan cigaban masarautarsu, jiharsu, dama kasarsu baki daya.
Bikin ya samu halartar masu ruwa da tsaki da suka hadar da shawagabannin kananan hukumomi takwas na masarautar, ‘yan majalissun jiha da na tarayya da kwamishinan ma’aikatar Safiyo Filaye da Gidaje na jihar Jigawa, Sagir Musa da mataimakin alkalin alkalai na kasa Gambo Sale, da tsofaffin shugabannin hukumar shige da fice da na yanzu daga sassa daban daban na kasarnan, da shugaban hukumar shige da fice na jihar Jigawa, da kuma “yan majalissar fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia.