Kwamitin Tantance Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC ya cire sunayen mutane 10 daga cikin mutane 23 da ya tantance domin yi wa jam’iyyar APC takarar Shugaban Ƙasa.
Shugaban Kwamitin Tantancewar, John Odigie-Oyegun, ne ya baiyana hakan a yau Juma’a.
Odigie-Oyegun ya yi bayanin ne lokacin da yake mika rahoton tantancewar ga Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu a Abuja.
Baya da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, da tsohon Gwamnan Jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu, sauran masu neman takarar Shugaban Ƙasar a APC da aka tantance sune; Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan da tsoffin ministoci; Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Godswill Akpabio, da kuma Chukwuemeka Nwajiuba.
Gwamnoni masu ci da aka tantance domin neman takarar sune; Kayode Fayemi (Ekiti), Yahaya Bello (Kogi), Dave Umahi (Ebonyi), Ben Ayade (Cross River) da Badaru Abubakar (Jigawa).
Sauran masu neman takarar sune; tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Ken Nnamani, tsohon Kakakin Majalissar Wakilai, Dimeji Bankole, da kuma sanatoci masu ci; Ibikunle Amosun, Ajayi Boroffice, da Rochas Okorocha.
Akwai kuma wanda ya taya Buhari takara a 2011 a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Pastor Tunde Bakare, Uju Ken-Ohanenye, Nicholas Felix, Ahmad Rufai Sani, Tein Jack-Rich, Ikeobasi Mokelu duk a cikin waɗanda aka tantance.
Oyegun ya baiyana cewa, mutum 13 ne kacal daga 23 suka sami tsallakewa a tantancewar kwamitin.
Ya bayar da satar amsar cewa, matasan cikin masu neman takarar ne suka sami tsallakewa amma ba tare da ya baiyana sunayensu ba.
Kamar yanda jadawali ya nuna, waɗanda aka tantance ɗin zasu kara a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC wanda za a gudanar a ranakun 6 da 8 ga watan Yunin da muke ciki.