For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Masu Rubuta JAMB Sun Je Jarabawa Da Wukake, Sun Yi Barazanar Maganin Shugabannin Jarabawar

Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB, ta ce masu rubuta JAMB sun yi amfani da wukake wajen yin barazana ga jami’an hukumar.

Zargin ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa, JAMB ta tabbatar da cewa, masu rubuta jarabawar da dama a Cibiyar Christ Ambassadors College, Sabon Tasha, Kaduna ba zasu samu damar rubuta jarabawar ba saboda matsalar na’urori.

Mai duba yanda ake jarabawar a cibiyar, Bilkisu Abdullahi, ta bayyana cewa, na’urar tura bayanan cibiyar ba zata iya daukar kwamfiyutoci 250 ba a lokaci guda kamar yanda aka tsara.

Jami’ar JAMB din ta kuma zargi iyayen masu zana jarabawar da rashin tabuka komai kan rikicin da ya taso.

Ta kuma shawarci iyaye da su nusar tare da koyar da ‘ya’yansu kyawawan halaye, inda ta kara da cewa, zuwa wajen jarabawa da wukake, abune da ba za a taba lamunta ba.

Bilkisu Abdullahi ta kara da cewa, masu rubuta jarabawar da ba su sami damar rubuta jarabawar a karon farko da na biyu ba, ana bukatarsu da su bayar da shedar rubuta jarabawar ga JAMB domin shirya musu yanda zasu yi jarabawar a nan gaba.

(NAN)

Comments
Loading...