For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Masu Sukar Buhari Game da Bashi, Marassa Gaskiya Ne – Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce wadanda ke sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari game da karbar bashi marassa gaskiya ne.

Ministan ya fadi hakan ne a ranar Alhamis a Maiduguri a wajen wani taro domin magance barnata layukan wutar lantarki da kayayyakin sadarwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa taron ya samu halartar Gwamnan Borno, Babagana Zulun, Mataimakinsa, Usman Kadafur, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewar ministan, gwamnatin Buhari ba ta na ciyo bashi ne don al’amuran yau da kullum ko biyan albashi ba, a maimakon haka tana ciyo bashin ne domin gina manyan ababen more rayuwa wadanda za su amfani ‘yan Najeriya.

Lai Mohammed ya ce suna da abubuwa da yawa da za su nuna wadanda aka yi da basussukan da aka karbo.

Cikinsu akwai dogayen layin dogo tsakanin Legas da Ibadan da Abuja da Kaduna wanda ya ce suna tafiya yadda ya kamata.

“A yau, muna da sabbin gyare-gyare a filayen jiragen sama a Abuja, Kano, Lagos da Fatakwal, akwai layin dogo na Itakpe zuwa Warri wanda aka yi watsi da su shekaru da yawa yanzu haka suna gudana.

“Muna da sama da kilomita 13,000 na titunan Najeriya da ake gyarawa da kuma sake ginawa kuma akwai irin wadannan aiyukan a kowace jiha.

“A yau, muna sane da lokacin kammala gadar Neja ta 2, wacce gwamnatoci daban -daban suka gina akan takarda kawai.

“Ayyukan da muke gudanarwa tare da bashin da muka ciyo suna da tsawo,” in ji shi.

Ministan ya ce abin mamaki ne yadda wadanda ke sukar gwamnatin suka yi abin da bai dace ba dangane da zamanantar da abubuwan more rayuwa na kasar lokacin da suke mulki a lokacin da samun kudin shiga ya ninka abin da ake samu a halin yanzu.

Ya ce da gwamnatin da ta gabata ta yi irin abubuwan more rayuwa da gwamnatin Buhari ta yi, da babu dalilin ciyo bashi yanzu.

Comments
Loading...