For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mata 6 Da Aka Zaba A Matsayin Mataimaka Gwamnoni Masu Jiran Gado A 2023

Cikin mata 24 da suka yi takarar neman zama mataimaka gwamna, 15 daga cikinsu sun kai ga shiga zabe tare da mazan da sukai musu takarar gwamna, yayinda shida daga cikinsu suka kai ga samun nasarar lashe zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan March da ya gabata.

A jihohi 28 wadanda aka gudanar da zaben gwamnoni a cikinsu, 15 daga cikinsu suna ‘yan takarar mataimaka gwaman mata a jam’iyya daya ko sama da haka, abin da ya sa adadin mata wadanda sukai takarar mataimakin gwamna ya kai 24.

Duk da kasancewar sakamakon jihohi biyu, Adamawa da Kebbi, cikin 28 da aka gudanar da zaben bai kammala ba, an riga an bayyana sakamakon jihohi 26, yayinda INEC ta shirya gudanar da sauran zaben da ya rage a Kebbi da Adamawa ranar 15 ga watan April, 2023.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, a jihohi 19 da ke Arewacin Najeriya, jihohi biyu ne, Kaduna da Plateau suke da mataimaka gwamna mata masu jiran gado.

Dr. Hadiza Balarabe Sabuwa, wadda likita ce, kuma ta kasance mataimakiyar gwamnan Kaduna tun 2019 ita ce mace ta farko da ta fara zama mataimakiyar gwamna mace a Jihar Kaduna, yanzu ma ta sake samun lashe zabe a matsayin mataimakiyar gwamna mai jiran gado a wa’adi na biyu.

Josephine Piyo ita ce mataimakiyar gwamna mai jiran gado a Jihar Plateau, inda ta samu nasara karkashin tutar jam’iyyar PDP tare da gwamna mai jiran gado, Caleb Mutfwang.

Dr Akon Eyakenyi ce mataimakiyar gwamna mai jiran gado a Jihar Akwa Ibom, inda ta samu nasara karkashin tutar jam’iyyar PDP wadda a yanzu haka kuma ita ce Mataimakiyar Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalissar Dattawa.

Dr Ngozi Nma Odu Farfesa ce a Jami’ar PAMO University of Medical Sciences, Port Harcourt, sannan kuma ta koyar a University of Port Harcourt sannan tana koyarwa a Rivers State Unkiversity a daidai lokacin da ta samu nasarar zama mataimakiyar gwamna mai jiran gado a Jihar Rivers.

Engr Noimot Salako Oyedele ita ce mataimakiyar gwamna mai ci kuma mai jiran gado a Jihar Ogun, kuma ita ce mace daya da ta zama mataimakiyar gwamna a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya kafin a bara a zabi Mrs Christianah Afuye a matsayin mataimakiyar gwamnan Jihar Ekiti.

Patricia Obila ta jam’iyyar APC ta zama mataimakiyar shugaban karamar hukumar Afikpo North a Jihar Ebonyi kafin a yanzu ta zama mataimakiyar gwamna mai jiran gado Hon Francis Ogbonnaya Nwifuru a jihar.

Comments
Loading...