For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mataimakin Gwamnan Anambara Ya Fice Daga APGA Ya Koma APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Larabar nan ya karbi mataimakin gwamnan Jahar Anambara Nkem Okeke daya sauya sheka daga jam’iyyar APGA zuwa APC a fadar shugaban kasar dake Abuja.

Mataimakin Gwamnan ya sauya shekar ne a makon daya gabata, inda shugaban kwamatin yakin neman zaben Gwamnan Anambara da za’ayi na ranar 6 ga watan Nuwambar dake tafe hadin gwiwa da gwamnan Jahar Imo Sanata Hope Uzodinma suka shige masa gaba wajen ganawa da shugaban kasar.

Uzodinma ya fadawa manema labarai na fadar shugaban kasa cewa “da sanyin safiyar yau ne Mataimakin gwamnan ya yanke shawarar komawa jam’iyyar ta APC”

Comments
Loading...