For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Matakai 11 Da Ya Kamata A Saka A Rai Kafin Shiga Al’amuran Siyasa

  1. Ba kowane dan siyasane kake a ransaba balle ya damu da rayuwarka ka sanda haka!
  2. Yan siyasa suna damuwa da biyan bukatar kashin kansune sama da bukatun mutanen da suke mulka.
  3. Mu’amala da yan siyasa tamkar kwana guri gudane da damisa; Dole ka ankare wajen yin bacci da, ido daya a bude da ya a rufe.
  4. A dukkanin lamuran yan siyasa sukan yi amfani da mutanene don cimma manufarsu musamman matasa, kaga kena kaima baka tsiraba ka kula.
  5. Yiwa yan siyasa aiki tamkar akan rauni ne, a duk lokacin da raunin ya warke bandejin ya gama aikinsa, da zarar sun dare madafun iko ka tashi aiki a gurinsu dan uwa matashi.
  6. Kada ka matsa sama da kima dan’uwa matashi a kan dan siyasa da zarar ya haye madafun iko zai tserene ya barka da tarin makiya shikuma yana can yana shan jarmiyarsa shida iyalansa.
  7. A cikin al’amuran rayuwa na siyasa ka dau zabinka wanda ka gamsu dashi ka ajiye tunanin wasu.
  8. Kada ka matsa wajen tsallaka kogi don yan siyasa, zaka iya nutsewa, abin da zasu iya shine aikawa da ta’aziya ga iyalanka, na romon baka don dan siyasa ba ya bin hanya don bawansa.
  9. Kada ka kashe kanka akan bukatunsu ko saka rayuwarka a rikici saboda dan siyasa dan’uwa, rayuwarka taka ce kai kadai ka san dadinta da akasin hakan.
  10. Sama da komi, a halinka da lafiyarka sune abubuwan da zan maka gargadi kada ka yi sake dasu, siyasa ba ta kyauta ta kaika ga wanna gabarba matashi.
  11. Abu na karshe yana da matukar hatsari ka salwantar da tarbiyarka, matakin karatunka, mu’amalolinka da mutuncinka don neman wani dan gajeran lada daga dan siyasa. Mu daure muso juna, mu kaunaci junanmu don lamuran siyasa na yau da zai sa ka ka zub da mutuncinka da kimarka cikin kankanin lokaci – tabonsa na iya binka har tarihin rayuwarka ya yi naso zuwa tsatsonka.

Musa Isma’il Birnin Kudu

Comments
Loading...