For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Matar Abdulmalik Da Ake Zargi Da Kisan Hanifa Ta Yiwa Kotu Bayanin Abun Da Ta Sani

Matar Abdulmalik Tanko mutumin da ake zargi da kisan Hanifa a Kano, ta bayyana a gaban kotu a ranar Alhamis da safe.

Jamila Muhammad Sani ta tsaya a gaban ƙuliya ne a matsayin mai bayar da shaida kan tuhumar da ake yi wa mijinta da sace tare da kashe yarinyar ƴar shekara biyar a watan Janairu.

Jamila ta amsa tambayoyi daga lauya mai gabatar da ƙara, Barista Musa Lawan, inda ta yi wa kotu bayani kan abin da ta sani game da zargin ɗauke Hanifa, wacce ɗaliba ce a makarantar da ta zam mallakin mijinta Abdulmalik.

Ta ce ya kawo mata yarinya ta tambaye shi ina iyayenta sai ya ce da ita uwar yarinyar ta sami aiki a Saudiyya, kuma ta tafi Abuja don cike wasu takardu.

“Amma har yamma na ga bai mayar da ita gida ba sai nake tambayarsa yaushe mahaifiyar yarinyar za ta dawo gida, kuma me ya sa har yanzu ba ta kira shi ba?

“Sai ya ce ba ta kira ba, daga baya sai ya ce sun yi magana da mahaifiyar yarinyar ta ce akwai layi ba za ta dawo ba a ranar ba,” in ji Jamila.

Ta ci gaba da bayyana wa kotu cewa bayan kwana biyu sai ya sake ce wa mata uwar yarinyar ta taho amma wani uzuri ya tsayar da ita a hanya, daga baya da ta sake tambayarsa, sai ya ce ta daina tambayarsa.

‘Yanda Na San Sunan Yarinyar’

Matar Abdulmalik ta ce ta kai ga sanin sunan yarinyar ne a tsawon kwanakin farko da kai Hanifa gidan, a lokacin da take kuka, ita kuma ta rarrasheta ta haɗa ta da ‘ya’yanta biyu don yin wasa.

Ta shaida wa kotu cewa yarinyar da ke jikin wani hoto da kotu ta yi wa laƙabi da hujja ta 5 lallai Hanifa Abubakar ce.

Sannan ta ce bayan kwana uku ta sake yi wa mijin nata Abdulmalik magana ya ce kudin mahaifiyar yarinyar ne ya ƙare tana Kaduna.

Amma saboda yadda ta matsa masa, sai ya faɗa mata cewar zai mayar da Hanifa wajen babarta.

Jamila ta ƙara da cewa a daren ranar na 5 ya sanar da ita zai mayar da Hanifa gida, a lokacin ta fara bacci, ya ce a ɗauko kayan makarantarta a saka mata.

Duk da ce masa da ta yi dare ya yi a lokacin 11 na dare, amma haka ya tafi kai ta a cewarsa.

“Lokacin da ya dawo na fara bacci, na kuma tambaye shi cewar ya mayar da yarinyar gida? Sai ya ce ‘e’.

“Bayan ƴan kwanaki sai na ga wata farar waya a hannunsa, sai na tambaye shi inda ya same ta sai ya ce min ta wani Hashimu Isyaku ce ya ba shi ya saka masa caji,” kamar yadda ta bayyana.

Tambayoyin Lauya Mai Kare Abdulmalik

Shi kuwa lauyan Abdulmalik wanda da ake ƙara Barista Muktar Labaran Kabo ya fara ne da tambayarta ko tana da rediyo da talabijin da take saurara?

Sai Jamila ta amsa masa cewar tana ji.

Ya sake tambayarta duk tsawon lokacin da Hanifa ke gidanta, ba ta taɓa jin cewar ana neman wata yarinya, ko maƙota su faɗa mata ana neman wata yarinya ba?

Sai ta ce masa ba ta saurarar rediyo sai dare shi ma shirin Karkaɗe Kunnuwa na Rahama kawai take saurara.

Ya tambayeta suna mahaifiyar yatinyar, sai ta ce Murjanatu sunanta.

Ya ƙara tambayarta ko tana da maƙota kuma tana zuwa wajensu? Sai ta ce tana da su, amma ba ta zuwa gidajensu sai da ƙwaƙƙwaran dalili.

Sannan ta ƙara da cewa “tun ranar Asabar ya kawo ta gida har zuwa ranar Alhamis” wato kwana biyar kenan.

Lauya Muktar Labaran Kabo ya tambayi Jamila ko tana da yaro mai shekaratakwas ko huɗu, kuma wacce makaranta yake zuwa?

Sai ta ce makarantar mai gidanta, wato inda Hanifa take kenan.

A ƙarshe lauyan ya tambayeta, ta ina ta sami labarin an sace Hanifa, duk da ta ce ba ta sauraren rediyo, sai ta ce ba ta taɓa ji ba sai sanda DSS suka gayyace ta.

Da waɗannan bayanai aka kammala karɓar shaidar Jamila.

Alkalin ya ɗaga sauraron ƙarar zuwa 9 da kuma 10 ga watan Mairs ɗin da muke ciki.

Waiwaye

A ranar wata Asabar 4 ga watan Disamban shekarar da ta ƙare ta 2021 ne aka sace Hanifa mai shekara biyar a unguwar Kawaji da ke birnin Kano.

Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku ko kuma A daidaita-Sahu.

Iyayen Hanifa sun ce mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.

“Babu nisa tsakanin makarantar da gidansu (Hanifa), saboda haka yaran sun saba zuwa da ƙafarsu,” a cewar Suraj Zubair, kawun Hanifa.

“Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce ɓarayin sun zo ne a A daidaita-Sahu kuma suka ce za su kai su gida.

Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita.”

(BBC HAUSA)

Comments
Loading...