For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Matar Aure Mai Ciki Ta Yi Garkuwa Da Kanta Ta Karbi Kudin Fansa Daga Saurayinta Na Facebook

An kama wata matar aure mai ciki da ake kira da Jamila Ardo saboda zargin yin garkuwa da kanta da karbar kudin fansa a wajen masoyinta.

Jamila, wadda ta fito daga garin Wauru Jabbe a karamar hukumar Yola ta Kudu da Jihar Adamawa, ta yi gangancin yin garkuwa da kanta tare da karbar kudin fansa naira miliyan 2 daga wajen Mallam Adamu Ahmed na Birnin Tarayya, Abuja.

Matar mai shekaru 25 a duniya, wadda ta hada kai da wani da ake kira da Abdulaziz wajen yin karyar garkuwa da ita da karbar kudin fansa, ta samu nasarar aiwatar da hakan.

An rawaito cewa ta yi amfani da kudin fansar ne wajen siyawa kanta gida.

Jamila da Malam Adamu sun fada cikin soyayya ne bayan sun hadu a kafar sadarwar zamani ta Facebook, ba tare da Malam Adamu ya san cewa yana soyayya da matar aure ba.

An gano cewar, tsawon lokacin da suka debe suna soyayya, masoyan ba su taba haduwa ido da ido ba, amma suna cigaba da soyayyarsu a yanar gizo.

Bayanan yanda akai damfarar, kamar yanda suke a karar da aka shigar sun nuna yanda Abdulaziz lokacin da yake hada baki da Jamila, ya kira Malam Adamu yana sanar masa cewa ya yi garkuwa da ita kuma ya bukaci kudin fansa.

A yayin da ake tattaunawa domin sakin Jamila, Malam Adamu ya ce ya jiyo Jamila tana kuka, tana rokonsa ta wayar da ya biya kudin fansar.

Malam Adamu ya sanya kudin fansar a wani asusun banki mai dauke da sunan Amina Mohammed.

Bayan ya tura kudin, Jamila ta kira masoyin nata inda ta sanar da shi cewar masu garkuwa da itan sun sake ta.

Malam Adamu ya shiga cikin rudani da zargi, inda ya shigar da kara Hukumar Binciken Asiri a ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2021.

Nan da nan jami’an bincike suka damke mamallakiyar asusun bankin wanda akai amfani da shi wajen karbar kudin fansar wato Amina Mohammed.

Bayan kamata, Amina ta amsa cewar kawarta Jamila ta nemi aron account dinta domin abokinta zai sako mata kudi.

Kafin wannan ta faru dai, mijin Jamila ya kalubalanceta kan kudaden da take samu, inda ta mayar masa da cewa ‘yanuwanta ne suke turo mata.

An kama Jamila tare da gurfanar da ita a gaban kotun majistare ta 1 da ke Yola kan zargin aikata babban laifi na garkuwa da mutane da kuma hada baki wajen aikata babban laifi, laifuffukan da suka saba da sashi na 60 da na 248 na kundin manyan laifuka.

To sai dai kuma Jamila ta musanta aikata laifin, yayinda dan-sanda mai shigar da kara, Sufeta Abubakar Nuruddeen ya nemi kotu ta dage sauraron karar domin ba su damar mika karar zuwa Directorate of Public Prosecution domin neman shawara.

Lauyan Jamila, C. Crowealth ya roki kotu da ta bar Jamila ta samu damar kulawa da lafiyarta duba da yanayin juna biyun da take dauke da shi.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya amince da bukatun lauyoyin, sannan ya dage cigaba da sauraron karar a ranar 10 ga watan Maris na wannan shekarar ta 2022, inda kuma ya ce a cigaba da tsare wadda ake zargin wato Jamila.

(PUNCH)

Comments
Loading...