Matar mataimakin shugaban kasa, Misis Dolapo Osinbajo, ta jaddada bukatar samun isasshen saka jari a ilimin yara mata don taimakawa wajen magance kalubale a cikin al’umma.
Misis Osinbajo ta bayyana hakan ne a cikin jawabinta a ranar ilimi ta gidauniyar MALLPAI ta 2021 wanda za a debe kwana biyu ana yi tare da taken: ‘Inganta Koyo don Ingantaccen Ilimi a Najeriya’ wanda ake yi a Abuja.
A yayin bikin, matar gwamnan jihar Kebbi, Aisha Bagudu, wacce kuma ita ce ta kafa gidauniyar Mass Literacy for Less Privileged and Almajiri Initiative (MALLPAI), ta ce isasshen saka hannun jari ga ilimin yara zai nisanta su daga fadawa aikata laifuka.
Da take bayyana ra’ayinta kan yadda ‘yan mata ke nuna kamar suna baya da maza, matar Osinbajon ta ce, akwai bukatar a kara kokari don cike gibin da ke tsakanin ilimin yara maza da na yara mata.
Ta ce: “Lokacin da yarinya ta samu ilimi, tana iya karatu da rubutu, ta san doka, kuma ta san soyayya. Lokacin da yarinya ke da ilimi, tana sane da irnin abubuwan da za ta iya cimmawa; za ta iya karanta tarihin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta Kungiyar Ciniki ta Duniya.”
Yarinya mai ilimi tana zaune akan kujera a Kebbi ko Kano, a Osogbo ko Oshodi, a Awka ko Uyo, tana fahimtar ka’idojin rayuwa kuma tana kara fadada hankalinta.
“Ku yi tunani, idan da Stella Adedavor, likita, ko Nana Asama’u, mawallafiya, a ce ba su taba samun ilimi ba.”
Misis Osinbajo ta yaba da kokarin da Gidauniyar MALLPAI ke yi na samar wa yara mata rayuwa mai ma’ana don cimma burin da suke so, inda ta yi kira da a kara himma don tabbatar da ilimi ga yara matan.
A jawabinta, matar gwamnan Kebbi Bagudu, ta bayyana cewa lokacin da gidauniyar MALLPAI ta fara da almajirai, ta fuskanci kalubale.
“Mutane ba sa ganin irin muhimmancin wadannan yara; kawai suna ganin abin haushi ne game da su. Amma mu muna ganin yaran, ba tashin hankali ba ne.
Ba ma raina irin wadannan yara, muna ganin su a matsayin mutane, har ma wasu daga cikinsu sun fara aiki, wasu kum suna aiki tare da Gidauniyar MALLPAI,” in ji ta.