Cincirindon matasa daga sassa ko bangarori daban-daban na jihar Jigawa, sun hade kai tare da yin amo iri daya wajen mika kokon bararsu ga senator mai wakiltar yankin Jigawa ta Tsakiya Distn. Sen. Sabo Nakudu.
Wannan roko kuwa ba komai bane, illa ganin dacewa da kuma cancanta da nagartarsa wajen neman kujerar Gwamnan jihar Jigawa a zabe mai zuwa na shekarar 2023.
Matasan sun gabatar da wadannan tarurruka ne a karkashin wasu kungiyoyi irin na matasa guda biyu masu suna kamar haka:
- Sen. Nakudu Social Media Team, karkashin jagorancin shugabanta Comr. Aminu Abbas Aujara, wadda ta gabatar da zamanta a babban ofishin ji da karbar koke na Senator Nakudu da yake babban birnin Jihar Jigawa, Dutse.
- Sen. Nakudu Consultation and Media Forum, wadda take karkashin jagorancin shugabanta Comr. Yakubu Dabi, wadda kuma ta gabatar da zamanta a ranar Lahadi 13/2/2022 a babban dakin taro na MDI da ke babban birnin jihar Jigawa, Dutse.

Dukansu matasan na Jihar Jigawa sun bayyana dalilansu kan wannan kira, inda suka ce, bai wuce yarda da amincewa da nagartar wannan bawan Allah ba, da kyawawan manufofin da yake da su, da kuma kokarin jan matasa a jika da yake yi a cikin tafiyarsa.
Fatan Allah Ubangiji ya kai fata mizani.
Abbas Musa Ladan Maikaras
Mataimaki Na Musamman Ga Sanata Sabo Nakudu kan Kafafen Yada Labarai