Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa ya karbi bakuncin wani taro kan nahiyar Afirka a Juma’ar nan.
Macron na ganawa kai tsaye da matasan nahiyar ta Afirka domin sauraren abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya.
RFI Hausa ta rawaito cewa, Shugaban Faransar, ya yaggayaci daruruwan matasa ‘yan kasuwa, masu fasaha da kwararru kan harkokin wasanni zuwa kudancin Montpellier, birnin da ake gabatar da taron.
Kamar yadda fadar Macron ta fitar da sanarwa, manufar taron ita ce, sauraren kalaman matasan Afirka da kuma neman mafita kan kalubalen da ke addabarsu.
Ganawar ta zo ne a wani lokaci mai cike da sarkakiya tsakanin Faransa da kwayayenta da suka yiwa kasashen Afirka mulkin mallaka, yayin da Faransar ke takaddama kan yanke shawarar hana takardun biza ga ‘yan kasashen Algeria da Morocco da Tunisia.
Algeria dai ta umarci jakadanta na Faransa ya koma gida, bayan da rahotanni suka ce Macron ya ce kasar na amfani da tsarin mulkin soja.