Wani matashi dan Najeriya mai suna Olowookere Victor Oluwaferanmi, ya bayyana irin nasarorin da ya samu a harkar karatunsa.
Victor ya bayyana nasarorin ta yanar gizo, inda ya tura sakon Twitter na hotonsa da hoton sakamakon WAEC dinsa na shekarar 2015 wanda ya ci ‘A’ takwas.
Wani hoton kuma yana nuna wasu daga sakamakon jarabawarsa ta karatun digiri a fannin fasaha inda kusan duk ya lashe jarabawar da ‘A’.
Da yake karin jawabi a hoton, Victor ya ce, ya samu nasarar kammala karatun digirinsa da maki mai darajar 4.8 cikin 5.0 CGPA.
Saboda nasarorin da yake samu, ya karbi shaidar girmamawa guda 9 tare da tallafin karatu.
Victor ya godewa Ubangiji kan nasarorin da ya samu, yayin da aka samu wata kungiya ta America na kokarin ba shi damar ci-gaba da karatu a America har matakin PhD.