For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

MATATAR DANGOTE: Babu Wani Tabbas Na Samun Sauƙin Farashi – NNPCL

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa ba shi da tabbacin cewa farashin man fetur zai ragu duk da fara ɗaukar mai daga matatar Dangote.

NNPCL zai fara ɗaukar man fetur daga matatar Dangote daga ranar 15 ga watan Satumba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Olufemi Soneye, ya fitar, ya bayyana cewa farashin kayayyakin man fetur daga kowace matata, har da Matatar Dangote zai dogara ne da yanayin kasuwannin duniya.

Soneye ya ce babu tabbacin cewa tace mai a cikin gida zai haifar da raguwar farashinsa.

Jawabin Soneye ya zo ne a lokacin da ake rade-radin cewa kamfanin yana yunkurin samun damar sayen dukkan albarkatun man da Matatar Dangote ke samarwa.

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmai ta MURIC ta yi zargin cewa canje-canjen farashin man fetur a baya-bayan nan zai hana Matatar Dangote damar sayar da mai a farashi mai rahusa, sannan NNPCL ya yi babakere zama wajen sayen mai daga matatar.

Comments
Loading...