For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Matsalar Rashin Jin Muhimmancin Kai

Daga: Aliyu M. Ahmad

Duk abin da yake 10 mallakinka ne, ya fi 1000 mallakin wani.  Hausawa na cewa, “zakaranka, rakuminka”; “kwai a baka, a fi kaza a akurki”, “kowacce kwarya, da abokin burminta”…

Ga wanda ya fahimci manufar rayuwar, ba zai jiyewa kansa ƙasƙanci ba, saboda dangi, dukiya, jinsi, ƙirar halitta, kalar fata, matsayi, ƙarfin kwakwalwa, muhalli, wayar hannu, abin hawa, kayan ƙawa (luxuries)… har kana hangen wasu sun fi ka.

Idan ka lura, muhalli da aka haifeka (ƙauye ko birni), iyayen da suka haifeka, jinsi, yanayin tattalin arziƙin gidanku, launin fatarka, harshenka, ƙabilarka, ƙarfin hazaƙar kwakwalwarka… ba laifin komai ka yi wa Ubangiji ya yi ka ƙasa da matsayin wasu ba; shi ma ɗan yallaɓai, ko ɗan ranka ya daɗe, ko ɗan Alhaji/hajiya, ko ɗan malam… ba shawara aka yi da shi ba, ya fito ta waɗancan tsatson ba, haka Allah Ya ƙaddara!

Ta fuskar addini, manufar rayuwa baki ɗaya, daga haihuwa zuwa muta ce, ka rayu, ka bautawa Allah. Duk wata daula, da gwagwarmaya, ana nema ne don samun nutsuwa, a yi ibada (bautawa Allah).

Manufar sutura, a rufe tsiraice ce, in dai ba tsirara ka ke tafe ba, saboda talaucin sutura; kai ma kana cikin sutura. Kar ka raina suturarka!

Manufar muhalli, wajen mu’amalar sirri ne, a kwanta a huta, da safe a fita neman halali. Bar ganin gidanku bai kai gida ba!

Manufar sana’a, a sami abin rufawa kai asiri ce. Ta fuskar neman halal, ba wata sana’a da ta fi wata; da gareji, office, bakin hanya, cikin kasuwa, shago… duk wurare neman halal ne; da lebura, ɗan kasuwa, ma’aikacin gwamnati… kowa fafutarsa na bin da za a rufawa kai asiri ne, a ci abinci, a yi sutura da muhalli, a biya buƙatun yau da kullum. Kada ka raina sana’arka.

Idan wani ya fi ƙoƙari a makaranta, wataƙila kana da wata baiwa, da shi ma ba shi da ita. Akwai masu nasara a makaranta, akwai masu nasara a rayuwar bayan makaranta. Wani ya yi nasara jiya, wani zai yi yau, wani nasararsa na zuwa gobe, mene ne na damuwa?

Manufar wayar hannu, a yi ƙira, tura SMS, email, browsing, ɗaukar hoto, chatting da reaction a social media, storing files, playing media… don Allah wayar hannunka ba ta wannan? Kada raina wayar hannunka!

Me ya sa za ka ji ƙasƙanci? Kai ma mutum ne, kana da daraja ta ɗan Adam. Ji wa kai ƙasƙanci na sa wa mutum rashin wadatar zuci, toshe basira, hana mutum sakewa, sa damuwa (depression), gina hassada a zuci, har kashe kai (suicide) ya ke jawowa (Alfred Adler, 1907). 

Idan kuma kana neman mai wauta, shi ne mai raina arziƙin wasu, ko jinsinsu, ko danginsu, ko matsayinsu, ko muhallinsu, ko wata ƙawa ta duniya (abin hawa, sutura, wayar hannu…).

Daga: Aliyu M. Ahmad

Comments
Loading...