Gwamnoni 19 na Arewacin Najeriya da sarakunan gargajiya na yankin sun bukaci da a yiwa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima domin bayar da damar samar da ‘yansandan jihohi.
Manyan na Arewa sun bayyana cewa, wannan ita ce kadai hanyar bi domin magance matsalar tsaron da addabi yanki da ma kasa baki daya, matsalolin da suka hada da na ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran matsaloli na tsaro.
Wannan kira dai na kunshe ne a cikin takardar bayan taro da aka fitar a karshen zaman Kungiyar Gwamnonin Arewa, NGF da Majalissar Sarakunan Arewa, NTRC wanda aka gabatar a daren ranar Litinin da ta gabata a Abuja.
An fitar da sakamakon tattaunawar ne a jiya, kuma wannan ne karo na farko da gwamnonin Arewa, tare da sarakunan gargajiya a Arewa suka gabatar da bukata mai karfi a kan samar da ‘yansandan jihohi.
Gwamnoni da sauran jagororin siyasa daga yankin Kudu, da kuma wasu ‘yan kadan daga Arewa a baya sun ta maganganu na kiraye-kirayen samar da ‘yansandan jihohi, al’amarin da akai watsi da shi saboda tsoron cewa idan aka samar da ‘yansandan jihohi wadanda suke biyansu zasu juyasu kan abokan adawarsu maimakon samar da tsaro.
Abun Da Shugabannin Arewa Suka Ce
Taron na ranar Litinin na manyan Arewa an yi shi ne a kan “Duba Yanayin Tsaro a Arewa a da Sauran Abubuwan da Suka Shafi Cigaban Yankin.”
Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamnan Jihar Plateau, Simon Bako Lalong; Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya; Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari; Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum; Gwamnan Jihar Niger, Abubakar Sani Bello; Gwamnan Jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku; da kuma mataimakan gwamnonin Adamawa, Benue, Nasarawa, da jihar Jigawa.
Sarakunan gargajiyar da suka halarci zaman sun hada da, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III; Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi; Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero; Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli; Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Idrissa; Sarkin Lafiya, Justice Sidi Bage Muhammad; Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad; Sarkin Gumi, Justice Lawal Hassan Gumi; Attah na Igala, Mathew Opaluwa; Ochi’ na Idoma, Pastor John Elaigwu; da kuma Uka na Wukari, Dattijo Manu Ishaku Adda Ali, da sauran wasu da dama.
Da yake karanta jawabin bayan taron bayan kammala taron da aka gudanar a Transcorp Hilton Abuja, Shugaban Gwamnan Gwamnonin Arewa, Lalong ya ce, an yi zaman ne domin a duba yanayin tsaro a Arewa da sauran abubuwan da suka shafi ci gaban yankin, sannan an amince da a goyi bayan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ta yanda za a samar da ‘yansandan jihohi.
Ya bayyana cewa, “Wannan zai matukar magance matsalar tsaron da ke addabar yankin,” in ji sanarwar bayan taron.