For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Matsin Rayuwa A Najeriya Na Neman Kayar Da Mutane, Tsarinka Na Bayar Da Tallafi Ba Mafita Ba ce – Abdussalam Ga Tinubu

Tsohon Shugaban Soja na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya nuna damuwarsa kan yunwa, talauci, da yanayin tattalin arziki da ke ƙara tabarbarewa a kasar, yana mai cewa lamarin na neman “ƙwacewa gwamnati.”

Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugabancin Ƙungiyar Yaƙi da Tauye Ƴancin Dan Adam a gidansa da ke Minna, Jihar Neja, inda ya nuna yanda ƴan Najeriya ke fuskantar ƙalubale wajen samun abincin ci da yin sufuri.

Ya ce hauhawar farashin sufuri, mai, kuɗin makaranta, da ƙarancin kuɗin da jama’a ke da shi na jefa su cikin mawuyacin hali, yana mai cewa kowa na ƙorafin wahalar rayuwa da ke ƙara tsananta a kullum.

Abdussalam ya bayyana cewa ya kasance cikin wata tawaga da suka miƙa shawarwari uku ga gwamnati kan yanda za a magance matsalar tattalin arziƙi, yana mai jaddada cewa tallafin da ake bayarwa ba zai iya zama mafita mai ɗorewa ba.

A cewarsa, ya kamata gwamnati ta sayi kayayyakin abinci ta rage farashi kuma ta sayar da su ga jama’a don rage matsin rayuwar.

Ya kuma yi kira da a gudanar da zanga-zangar lumana a yayin da ake shirye-shiryen gangamin #EndBadGovernance a ranar 1 ga Oktoba, yana mai jaddada bukatar guje wa tarzoma kamar yanda ta faru a zanga-zangar baya.

Comments
Loading...