Shaharren mawakin nan Davido, ya cika alkawarin da ya dauka na bayar da tallafin naira miliyan 250 ga gidajen marayu 292 a jihohi 27 daga jihohin Najeriya.
Karasa kammala cika alkawarin ya faru ne kwanaki 89 bayan mawaki Davido ya baiyana aniyarsa ta tallafawa gidajen marayu a fadin Najeriya.
Mawaki Davido wanda ya samu lambobin yabo da dama, ya sanar da cewa, kwamiti mai mutane biyar da ya kafa a watan Nuwamban 2021 domin tattaro sunaye da bayanan gidajen marayu masu rijista, ya kammala mika tallafin ga gidajen marayun.
A wallafe-wallafen da yai a daren jiya Talata a kafar Twitter, Davido ya bayyana dukkanin sunaye da kuma guraren da gidajen marayun da suka mori tallafin suke.
