For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mazaɓun Sanatoci 6 Da Ba Su Taɓa Yin Gwamna Ba Tun 1999

Binciken da DAILY TRUST ta yi ya nuna cewar akwai aƙalla mazaɓun sanatoci guda 6 a Arewacin Najeriya da ba su taɓa fitar da gwamna a jihohinsu ba tun dawowar mulkin demokaraɗiyya a shekarar 1999.

Mazaɓun sune, Mazaɓar Benue ta Kudu, Mazaɓar Kwara ta Arewa, Mazaɓar Kogi ta Yamma, Mazaɓar Borno ta Kudu, Mazaɓar Adamawa ta Tsakiya da kuma Mazaɓar Yobe ta Arewa.

Mafi ƙarfin magana a kan dalilin ya hana waɗancan mazaɓu ita ce, rashin yawan jama’a a mazaɓun, tun da ita demokaraɗiyya tsari ce da mai jama’a ke wucewa gaba, to sai dai kuma, mutane na nuna buƙatar a samar da gyara a tsarin ta yanda marassa rinjaye ma zasu na samun damar ana damawa da su.

Matsalolin Da Ake Dangantawa Da Mazaɓa:

Mazaɓar Adamawa ta Tsakiya

Wannan mazaɓa tana da ƙananan hukumomin biyar ne da suka haɗa da Madagali, Michika, Maiha, Mubi ta Arewa da kuma Mubi ta Kudu.

Babban ɗan Jam’iyyar APC, Sanata Abubakar Halilu Girei ya bayyana rashin jagoranci, haɗin kai da samun manufa a matsayin abun da ya hana wannan mazaɓa samun damar fitar da gwamna a Adamawa.

Mazaɓar Yobe Ta Arewa

Wannan mazaɓa na da ƙananan hukumomi guda shida da suka haɗa da, Jakusko, Bade, Yusufari, Karasuwa, Machina da kuma Nguru.

Wani tsohon ɗan takara a jami’iyyar PDP, Auwal Kaska Yusufari ya bayyana biyayya da mazaɓar take da shi ga jam’iyya marar rinjaye a matsayin dalilin da ya hanata samun damar fitar da gwamna a jihar ta Yobe.

Ya ce, jam’iyyar PDP ta gwada Baba Gwani Machinaa 1999, Usman Albishir a 2007 da kuma Shareef Abdullahi a 2023 daga mazaɓar amma dukkansu babu wanda ya ci zaɓe.

Ya ƙara da cewar akwai alamun cewar, mutanen Yobe sun yarda kawai iya ɗan takarar jam’iyyar gwamnati ne zai iya cin zaɓe, shi yasa duk lokacin da PDP ta ba wa nasu takara ba sa dagewa yanda ya kamata.

KARANTA WANNAN: El-Rufai Ya Haƙura Da Muƙamin Minista, Ya Tura Sunan Madadinsa

Mazaɓar Benue Ta Kudu

Wannan mazaɓa tana da ƙananan hukumomi takwas ne waɗanda mafi yawancin su ƴan ƙabilar Idoma ne, sun haɗa da, Otukpo, Ohimini. Okpokwu, Agatu. Apa, Oju, Obi da kuma Ogbadibo.

Muƙamin gwamna a Jihar Benue na ta yawo ne a tsakanin ƴan ƙabilar Tiv waɗanda suke a sauran mazaɓu biyu na sanatoci a jihar.

A lokuta da dama, ƴan ƙabilar Idoma sun roƙi ƴan ƙabilar Tiv da su bar su su ma su fitar da gwamnan jihar daga cikinsu, to amma har kawo yanzu Tiv ba su yarda muƙamin gwamnan ya suɓuce daga hannunsu ba.

Mazaɓar Kwara Ta Arewa

Wannan mazaɓa na da ƙananan hukumomi guda biyar da suka haɗa da Patigi, Edu, Baruten, Kaiama da kuma Moro.

Manya daga wannan mazaɓa sun bayyana rashin haɗin kai da babbancin siyasa a matsayin dalilin da suka hana yankin samun damar fitar da gwamnan jihar tsawon shekaru.

An rawaito cewar, a shirye-shiryen zaɓen shekarar 2019, sarakunan gargajiya da ke mazaɓar sun samu yarjejjeniya da Dr. Bukola Saraki kan cewar PDP zata fitar da ɗan takara daga yankin, abun da ya sa a shekarar 2023 PDPn ta bai wa Alhaji Shuaib Yaman daga ƙaramar hukumar Edu damar yin takara, amma a ƙarshe bai ci zaɓen ba.

Mazaɓar Kogi Ta Yamma

Wanna mazaɓa na da ƙananan hukumomi bakwai da suka haɗa ake ƙabilun Yarabawa, Igbura, Nupe da Kankanda a cikinsu.

Ana alaƙanta dalilin rashin samun damar mazaɓar na yin gwamna tsawon shekaru da kasancewar ƙabilun da ke yankin sune tsirarun ƙabilu a jihar ta Kogi, sannan kuma akwai rashin haɗin kai a tsakaninsu.

Mazaɓar Borno Ta Kudu

Wanna mazaɓa na da ƙananan hukumomi 9 cikin 27 na jihar waɗanda suka haɗa da Askira Uba, Bayo, Biu, Chikok, Damboa, Gwoza, Hawul, Kwaya Kusar da kuma Shani.

Manyan ƴaƴan jam’iyyun PDP da APC a Jihar Borno sun yarda cewar, ƙabilanci, banbancin addini da ƙarancin jama’a sune suka taka muhimmiyar rawar da ta hana mazaɓar yin gwamna a Jihar Borno.

A ko da yaushe mazaɓu biyun su kan haɗe kansu a kan Mazaɓar Borno ta Kudu saboda addini da kuma ƙabilanci.

Comments
Loading...