For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mece Ce Wayewa?

Daga: Aliyu M Ahmad

Cikin gajerun kalmomi, WAYEWA na nufin “sanin daidai” ko “fahimtar (manufar) rayuwa”; WAYAYYEN MUTUM (civilized) shi ne “mai sanin ya kamata”, da “aikata daidai a lokacin da ya dace” akasin wayewa, shi ne GIDADANCI, ko ƘAUYANCI.

Ibn Khaldun cikin Muƙaddima (p. 102), kalmar ‘wayewa’ ba ta taƙaita ga mutum ɗaya ba, an fi danganta ta ga al’umma da zamantakewa. A baya, an yi al’ummomi da suka rayu daga ‘badawa’ (rayuwar ƙauye) zuwa ‘hadara’ (rayuwar birni da wayewa) cikin cikakken tsari daidai da zamaninsu; misali, daulolin Girka, Rum, Misra, Maya, Minoan, Aztec, Farisa… zamanin daulolin Musuluncin (Islamic Golden Age), zamanin su Khalifa Haruna Rashid, Baibars…

Wayewa tana da alaƙa da tsarin rayuwa; ilimi, wurin zama, siyasa, adalci, addini, harshe da al’adun mutane. ‘Ilimi’ ko ‘shekaru’ ko ‘matsayin tattali’ ko ‘wurin zama’ (ƙauye ko birni), ba sa nuna mutum wayayye ne ko gagidaje, sai dai suna da tasiri kan hakan. Haƙiƙar wayewa na cikin tunani da mu’amala. Akan iya samun ɗan birni bagidaje, a iya samun wayayyen mazaunin ƙauye. Wayewa a wata al’umma na shan-bamban da ta wata.

Amma ta fuskar baki ɗaya (general):

Wayayye shi ne wanda ya fahimci manufar halittarsa da rayuwarsa, sannan ya yi ƙoƙarin rayuwa don ɗabbaka hakan. Wayayye ba ya aikata wani aiki, ba tare da sanin hukuncin addininsa, ko dokar ƙasarsa a kai ba.

Wayayye shi ne wanda ya fahimci tsarin muhallin da yake rayuwa (mis. Nijeriya, tsarin siyasarta da dokokinta, da yanayin al’ummarta; wannan ya sa ake karantar da mutane ‘Civic Education’ a makarantu).

Wayayye na da hangen nesa da kyakkyawar ɗabi’a, duk inda ya shiga, zai zauna da kowa lafiya, ya yi mu’amala mai kyau hatta ga waɗanda suke da bambanci ƙabila, harshe, addini ko a matsayi ba tare da nuna fifiko, ko tsarkake kai ba [Tafsir al-Sa’di, p. 856].

Ta fuskar ilimi, yana karatun addini da boko daidai gwargwadon buƙata (yana da ido a zamanance da addini; don kar a layince masa, ko bautar da tunaninsa, ko halarkar da shi, ko a cuce shi). Wayayye yana magana ta ilimi a abin da ya sani na ilimi ko labari, ko zamantakewa (a lokacin da ya dace), ba ya shiga fannin da ba na sa [Tasfir al-Sa’ady p. 457 & Al-Jawab Al-Kafi 1/8].

Wayayye yana tafiya daidai da zamani, ba tare da jefar da tsarin addininsa, da al’adarsa mai kyau ba. Ba ya raina halittarsa, ko jin ƙasƙanci a karan kansa [Suratul Hujurat, 13].

Wayayye yana riƙe mutuncin kansa, baya shiga sabgar da ba ta shafe shi, ba ya sa ido wa rayuwarsu, sabgogin gabansa ya sa a gaba. Wayayye na ƙoƙarin gano baiwarsa, yana rayuwa da manufa, ba don burge mutane ba. Ya kan siyan abu don amfanin da kansa, ba ya gasa da kowa, balle hassada. Ba ya jayayya, ko maganganun marasa amfani [Al-Hujurat, 12].

Wayayya mai tsafta ne, baya zama da ƙazanta, ko warin jiki. Ba ya ado, ko takurawa kai da kayan ƙawa don burge mutane [Muslim, 9].

Wayayye ba ya girman kai (ƙin gaskiya, jiji da kai, da raina mutane). Baya gorin ni’imar arziki, dangi, muhalli, addini, domin ya san Allah ne Ya ni’imta shi, ba wayonsa ba. Wadatar zuci, babbar alama ce ga wanda ya fahimci manufar rayuwa.

Wayayye ba ya yi wa wani, abin da in aka yi masa, shi ma; zai ji ba daɗi. Wayayye ba ya zagin iyaye, ko malamai, ko addini, ko abin bautar wasu; domin ya san aikata hakan, daidai yake da zagin nasa iyayen, malaman, addini da abin bauta; a ramko [Ibn Kathir 3/314].

Wayayye yana yi wa kowa adalci, baya goyon bayan ƙarya ko da a kan kansa ne, ko da ga makusantansa ne [An-Nisa’i, 135].

Wayayye ya fahimci dukkan mutane suna da alaƙa da juna, duniya muhallin kowa ce, abin da ya shafi mutumin Gabas, ya shafi mutanen Yamma. Misali, COVID-19 da fara daga China (gabas), ta haɗe kudu, arewa da yammancin duniya. Bala’in yaƙin Ukraine da Russia, ya haɗe farashin abinci na duniya. Yaƙin Gabas-ta-Tsakiya (Mid-East), ya yi nason ta’addanci, har a nan Nijeriya. Ambaliyar ruwa wasu garuruwa, za su shafi tsadar abinci a shekara mai zuwa.

BABU WAYEWA CIKIN SAƁON ALALH! Ba wayayye ba ne, mai ganin shaye-shaye, zina, zuwa gidan rawa da party, ko kwaikwayon al’adu marasa kyau.. a matsayin wayewa, ISKANCI ne, da GIDADANCI, saboda ya saɓa da addinsa, al’adarsa, da ɗabi’un mutanen kirki.

✍️ Aliyu M. Ahmad

Comments
Loading...