Ministan Kwadago da Samar da Aikin Yi, Dr. Chris Ngige ya zargi malaman jami’a da makala son zuciyarsu a kan Gwamnatin Tarayya domin su sami tausayawar ‘yan kasa kan shirinsu na shiga yajin aiki.
Dr. Ngige ya ce, gwamnati tana cika alkawuran da ke cikin yarjejeniyar shekarar 2020 wadda aka yi da shugabancin ASUU.
Ministan yana mayar da martani ne ga malaman jami’o’in da suke barazana jefa jami’o’in gwamnati cikin halin yajin aiki domin kalubalantar alkawuran da ba a karasa cikawa ba.
Malaman Jami’ar sun baiyana cewa cika alkawarin da akai musu a shekarar 2009 ne kadai zai dakatar da su daga tsunduma yajin aikin.
Dr. Ngige ya ce gwamnati ta saki kudi naira biliyan 70 a shekarar 2021 na gyaran jami’o’in gwamnati (naira biliyan 30) da alawuns din koyarwa (naira biliyan 40) domin nuna mutumtawarta ga yarjejeniyar da akai.
Ministan ya ce, “Ba gaskiya ba ne. Sun karbi alawuns din su na koyarwa na 2021. Yana gaba-gaba a kasafin kudin shekarar 2021 kuma sun karbe shi.
“Mun biya naira biliyan 22.72 wanda aka ware a kasafin 2021. Kuma sun karbi na 2020 sun raba shi a tsakaninsu da sauran kungiyoyi. Sun same shi a watan Janairu na 2021.
“Lokacin da suka janye yajin aiki a watan Disamba na shekarar 2020, kudin yana cikin yarjejeniyar da akai. An biyasu naira biliyan 40 na alawuns din koyarwa da kuma naira biliyan 30 na gyaran jami’o’in gwamnati a farkon shekarar 2021, wanda ya kama naira biliyan 70.
“Idan kuma sun ce babu EAA a Kasafin Kudin 2022, me yasa ba za su jira a fitar kwarya-kwaryar kasafi? Akwai tsari da ya kamata mu duba. Wannan tsari yana iya canzawa duk shekara kuma ofishin kasafin kudi yana duba shi.