Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, yana fuskantar suka bayan da aka danganta shi da ƴan ta’adda.
Ana zargin Matawalle da sayawa shugabannin ƴan ta’addar motoci, ciki har da shahararren jagoran ƴan bindigar, Bello Turji da wasu ma, lokacin da yake gwamna a jihar Zamfara.
Gwamnan jihar mai ci yanzu, Dauda Lawal ne ya bayyana hakan a gidan talabijin na TVC ranar Laraba inda ya yi kira ga Matawalle da ya yi murabus daga kujerarsa ta
Lawal ya ce da shi ne Matawalle, da ya ajiye aiki don ya fuskanci tuhumar da ake yi masa ta alaƙa da ƴanta’adda.
A cewarsa, tsohon gwamnan yana haduwa da ƴan bindiga a gidan gwamnati kuma an biya kuɗin fansa ta hannun gwamnatin jihar a wancan lokacin.
Lawal ya ƙara da cewa EFCC tana bincike kan zargin almundahana da ta kai ta naira biliyan 70 tun watan Mayun shekarar 2023.
Wakilin fadar shugaban ƙasa da aka miƙawa tambaya kan waɗannan zarge-zarge ya ƙi yin tsokaci kan batun, yana mai cewa amsa zata fito nan ba da dadewa ba.
Wannan dai ba shine karo na farko da ake zargin Matawalle da tallafawa ƴ.an bindiga ba.
A watan Janairu shekarar 2022, PDP ta kira gwamnan da ya yi murabus kan zarginsa da hannu a aikata ta’addanci.
Haka kuma, malamin addinin Musulunci, Bello Asada, ya yi ikirarin cewa Matawalle ya sayawa shugabannin ƴan bindiga mota.
Asada ya tambayi dalilin da yasa ba a kama Turji ba, duk da kasancewarsa shahararren ɗan ta’addar da yai shuhura a kafafen sada zumunta.
A lokacin gwamnatinsa a Zamfara, Matawalle ya yi afuwa ga ƴan bindiga, wanda Turji ya zargin cewa da goyon bayan wasu daga cikin ƴan uwansa aka aikata hakan.
To sai dai kuma, wani mataimaki ga Matawalle ya musanta zargin, yana mai cewa Gwamna Lawal na neman ɓata masa suna ne kawai.
Mai sharhi kan al’amuran tsaro, Kabir Adamu, ya bayyana cewa wannan zargin na nuna yanda aka sanya siyasa a harkar tsaro a Najeriya.