For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ministar Kudi Ta Zargi Masu Fasakwauri Da Jawo Tsadar Shinkafa A Nigeria

Daga: Kabiru Zubairu

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana cewa fasakwaurin da ake na shigo da shinkafa cikin Najeriya shine ke kara ta’azzara tsadar shinkafa a kasar.

Ministar ta bayyana hakan ne jiya Alhamis a tattaunawarta da gidan talabijin na Channels a cikin shirin Politics Today inda ta ce fasakwaurin na cutar da kasuwanci wanda hakan kuma ke cutar ‘yan kasa.

“Abin takaicin shine, akwai matsalolin tsaiko da ake samu, kuma wadannan matsaloli na tasowa ne daga bangaren fasakwaurin kayayyaki da ake zuwa cikin kasar,” in ji Ministar.

“Muna da ‘yan Najeriya marassa kishi da ke shigo da shinkafa marar kyau, wata ma ba ta dace da cin dan’adam ba, su zo su ajjiye ta a kasauwa.”

Ministar ta bayyana kokarin da gwamnantin tarayya ke wajen ganin cewa an magance matsalar fasakwaurin, inda ta ce akwai rundunar hadin guiwa da ta hada da jami’an Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Najeriya, Jami’an ‘Yansanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya da sauransu domin fuskantar matsalar masu yiwa tattalin kasa zagon kasa.

Comments
Loading...