For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ministoci 8 Da Ƴan Najeriya Ke Mamakin Muƙaman Da Tinubu Ya Ba Su

Duba da yanayin aiki da karatun da waɗanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura wa Majalissar Sanatoci domin tantancewa, ƴan Najeriya ciki har da su kansu sanatocin, sun yi tsammani daban da abun da suka gani a matsayin muƙaman da shugaban ƙasar ya ce ya bai wa da dama daga cikin sabbin ministocin.

Badaru Abubakar – Ministan Tsaro

Duk wanda yake da CV irin na tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar, za a yi tsammanin a ji shi a ma’aikatu irin na kasuwanci, tattalin arziƙi ko noma, amma cikin mamaki sai ƴan  Najeriya suka ji sunansa a matsayin Ministan Tsaro, bayan kuwa a tarihinsa ko ma a tambayoyin da sanatoci suka so yi masa babu maganar yanda za a samawa ƙasa tsaro, saboda sun san cewar wannan ba fanninsa ba ne.

Adedayo Adelabu – Ministan Lantarki

Duk wanda yake da CV irin Adebayo Adelabu wanda kafin naɗinsa yai aiki a matsayin mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, za a yi tunanin cewar zai samu ma’ikatu irinsu ma’aikatar kuɗi ko ta kasuwanci, amma kwatsam sai ga shi yana jiran rantsuwa a matsayin Ministan Lantarki.

Dele Alake – Ministan Bunƙasa Ma’adanai

Inda ƴan Najeriya ne ke da zaɓin bai wa Dele Alake ma’aikatar da zai jagoranta a matsayin minista, to da alamu ta Yaɗa Labarai zasu zaɓa masa saboda a nan ƙwarewarsa take, to amma da yake lamarin ba haka yake ba, Shugaba Tinubu ke da wuƙa da nama, sai ya ba shi Ministan Bunƙasa Ma’adanai.

Lola Ade-John – Ministar Harkokin Yawon Buɗe Idanu

Lola Ade-John dai ƙwararriyar masaniyar harkokin fasahar sadarwa ta zamani ce, sannan kuma ta yi aiki na tsawon shekaru a ɓangaren banki, saboda haka ne ma sanatoci a lokacin tantance ta suka mayar da hankali kan abun da ta ƙware a kai da tunanin cewar a nan ɓangaren zata taya shugaban ƙasa aiki, amma cikin mamaki sai aka ji sunanta a matsayin Ministar Harkokin Yawon Buɗe Idanu.

Festus Keyamo – Ministan Bunƙasa Harkokin Jiragen Sama

Shi dai Keyamo shi ne tsohon Ƙaramin Ministan Ƙwadago kuma Babban Lauyan Najeriya ne, saboda haka za a yi tunanin ko ya koma tsohuwar ma’aikatarsa ko kuma wani waje da yake da tarihin samun ƙwarewa a kai, amma kuma Tinubu ya miƙa shi ɓangaren Jiragen Sama.

Abubakar Momoh – Ministan Matasa

Naɗin dattijo Abubakar Momoh ɗan shekara 63 a duniya a matsayin Ministan Matasan Najeriya ya zo wa ƴan Najeriya da matuƙar mamaki, abun jira dai a gani shi ne ko zai iya kulawa da matasan a shekaru ukun da yake da su masu zuwa.

Nyesom Wike – Ministan Babban Birnin Tarayya

Nyesom Wike wanda ɗan yankin Kudu maso Kudancin Najeriya ne, kuma tsohon Gwamnan Jihar Rivers, duk da an yi surutai kan ba shi muƙamin minista a gwamnatin APC kasancewarsa ɗan PDP, amma kuma ana samun nutsuwa idan aka tuna cewar ya taya Bola Tinubu wajen cin zaɓe.

Amma kuma tunani mafi yawa kan muƙamin da za a ba shi na kan cewar zai samu muƙamin Ministan Niger-Delta, ba a taɓa tunaninsa a matsayin Ministan Abuja ba, musamman ganin kasancewarsa ɗan Kudu, kuma tun dawowar mulkin demokaraɗiyya a 1999 ba a taɓa samun wanda ba ɗan Arewa ba a muƙamin.

Bello Matawalle – Ƙaramin Ministan Tsaro

Ba a taɓa tsammanin cewar Matawalle zai samu aiki a ɓangaren da ya gagare shi tsawon kasancewarsa gwamna a Jihar Zamfara ba.

Comments
Loading...