Gina cikakkiyar jam’iyya mai haɗin kai shi zamu sa a gaba, in ji Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki, Sanata Abdullahi Adamu a jiya Lahadi.
Ya ce sabbin shugabannin jam’iyyar zasu fara samar da daidaito na gaskiya domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2023.
A jawabinsa, jim kadan bayan ƙaddamar da shi, Adamu ya ce, dole ne dukkanin ƴan jam’iyyar su yi aiki wajen samar da haɗin kai indai ana son jam’iyyar ta yi nasara.
A dai jiyan, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce, haɗin kan da ƴan jam’iyyar suka nuna a taron da aka yi a ƙarshen mako, zai tabbatar da nasarori a gaba matuƙar an ci gaba a haka.
Ya kuma taya sabbin shugabannin murna, inda ya ce samuwarsu “nasara ce a kan masu cewa a’a.”
A ɓangarensa, sabon shugaban Adamu, ya yi gargaɗi kan nuna halin nunƙufurci wanda zai iya yiwa jam’iyyar illa.
Tsohon gwamnan Jihar Nasarawan ya kuma ce, “Mun karbi aiki guda da kuka dora mana a kafaɗunmu.
“Zamu yi aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa mun yi abun da babbar jam’iyyarmu da ƙasarmu suke fata akan mu.
“Ina son kuma in taya murna ga manyan mutanen jam’iyyarmu maza da mata waɗanda suka nemi wannan matsayi a matakin ƙasa a wannan babbar jam’iyyar tamu.
“Ba su sami nasara a wannan lokacin ba, amma a lokacin da Allah Ya so, da yawansu zasu damar yiwa jam’iyyarmu hidima da ma ƙasarmu baki ɗaya.
“A matsayinmu na ƴan siyasa, mu ba baƙin samun nasara, faduwa da jin kunya ba ne a sakamakon takarar siyasa.
“Ya kamata mu nuna dattako da kuma kishi, mu karɓi sakamakon wannan zaɓe da girmamawa.
“Jam’iyyarmu tana buƙatar gudunmawar kowa wajen tafiyar da ita, ta haka ne zamu tuƙa jirginta ya ratsa duhu da surƙuƙin siyasar ƙasar nan zuwa ga nasara.
Abdullahi Adamu ya baiyana cewa jam’iyyar PDP ta ji kunya ganin cewa APC ta samu nasarar zaɓen shugabanninta na ƙasa.
Ya yi gargaɗi game da rigingimun daidakun mutane kar a bari su zama rigingimun jam’iyya gaba ɗaya.