A ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairun 2022, fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi ta saki wata takarda ta shafin ta na Instagram dangane da rikicin da ya ke ta ballewa a masana’antar Kannywood.
Jarumar ta nuna rashin jin dadin ta dangane da yadda kace-nace yake ta aukuwa a masana’antar har ta kai ga ana zargin mata da bayar da kawunan su kafin a sanya su a fim.
A cewarta, tana cikin jarumai mafi tsada, kuma bata taba bin wani furodusa ko darekta don ya sanya ta a fim ba, su da kan su suke bin ta.
A cewarta, tana shimfida musu dokokin da sai sun bi kafin ta shiga fim din su.
Don haka ta shawarci matan Kannywood ta su tsare mutuncin su kuma su fallasa duk wanda ya neme su.
Jarumar ta yi wannan rubutun ne bayan Naziru Ahmad, Sarkin waka ya zargi wasu darektoci da furodusoshin masana’antar da neman jaruma mace kafin su sanya ta a fim din su, zargin da Nafisa ta kira ‘mara tushe balle makama’.
A takardar wacce ta saki da harshen turanci kamar yadda LabarunHausa.com ta ruwaito, ta ce:
“Amincin Allah ya tabbata a gare ku.
“Duk wanda yake bibiyar abubuwan da suke faruwa a masana’antar mu ta Kannywood zai fahimci cewa muna ta durkusar da kawunan mu ne maimakon dunkulewa don gina masana’antar. Abin ban takaici.
“Dangane da tarin zargin da ake ta yi marasa tushe balle makama musamman yadda muka tattara muke yi wa maza kudin goro kamar yadda wani dan uwan mu wanda bai san abubuwan da suke faruwa kusa da nesa da shi ba a Kannywood ya tattara ya yi wa mata kudin goro akan cewa suna bayar da jikin su don a daura su a fim. Wanne irin tunani ake so mutane su yi?
“Idan kana so ka zargi mutane, ka tabbatar kana da hujjar da zata tabbatar da zargin ka.
“Ina so in fadi wannan maganar, idan kana da wata matsala da wani, ka kira sunansa don ku tattauna akan matsalar, amma kada ka yi surutai duk don ka birge jama’a sannan ka bata sana’ar ka da rayuwar ka gabadaya.
“Ina cikin jeri ko kuma cikin jarumai mata mafi tsada a na masana’antar Kannywood kuma ban taba bin wani don ya sanya ni a cikin fim din shi ba, zuwa wurina suke yi.
“Ban kai wannan matakin ba ta hanyar bin dokokin wani, ni nake sanya dokoki na, idan kuma kina iya yin komai duk don a sa ki a wani aiki, a haka zaki kare in har baki gina kan ki ba.
“Ki yi aiki na gaskiya da gaskiya, tabbas za ki ci moroyar hakan.
“Ina kara fadi, ba zan yi musu da wani dangane da zaton da yake yi wa matan masana’antar nan tamu ba, gaskiyar magana ita ce in har kika yi kokuwa da alade, duk za ku yi datti, amma dama shi alade haka yake so.
“Kuma abin takaici dangane da zamanin nan shi ne yadda mugayen mutane suke cutar da mutanen kirki. Kuma ina kira ga matan masana’antar mu akan in har kina so ki sauya wani abu, wajibi ne ki yakice duk abubuwan da suke dakatar da sauyin da kike son yin.
“In har an taba neman ki bayar da kan ki don a daura ki a wani matsayi a fim, ki jajirce ki kira wanda ya taba neman ki in har da gaske ne.
“Amma gaskiya mu daina zargi mara tushe balle makama sannan mu daina yi wa kowa kudin goro.
“In har muna da wata matsala da wani, kamata ya yi mu zauna teburin sasanci da shi, ba mu lalata komai ba, ba tare da sanin yadda zamu gyara shi ba.”
(LabarunHausa)