Sakamakon juyin-mulki da sojoji sukayiwa ‘yan siyasa da canja kundin tsarin mulki da kwace siyasa da sojoji masu kazamin laifi sukayi daga hannun ‘yan siyasa farar-hula, masu mutunci da imani, masu tsoron Allah da tausayin bayin Allah Najeriya ta shiga wani irin hali na rashin imani. Daga sata sai kisa sai fajirci da kowanne irin sabon Allah ba hukunci.
Sojoji suka zama ‘yan fashi da ‘mukami’, suka haifar da masu yin fashi da makamai da fyade da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa da ‘yan fashin daji. Babu noma babu kiwo babu sana’o’in hannu babu fatauci sai jiran mutuwa.
Shugabanni sun gaza ko sunki tsare rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na ‘yan kasa da baki da masu shigowa cikin kasar. Komai ya tsaya cik! Idan munkasance masu hankali da ilimi bai kamata mu kasa daukar matakan kawarda miyagun shugabanni irin wadannan ba, wadanda ba ruwansu da Allah sai kudi.
Idan mukayi waiwaye can baya, shugabannin siyasa ba haka suke ba. Masu akida da kaunar ‘yan uwa da son cigaban al’umarsu da kasarsu ne suke haduwa su kafa jam’iyyar siyasa, su raya ta harta bunkasa, su zabi wadanda sukafi cancanta da dacewa su wakilcesu a mukamai daban daban, tundaga kananan hukumomi zuwa jihohi da tarayya har izuwa wadanda ake nadawa bisa cancanta da dacewa, wadanda zasu iya fahimtar duk abubuwanda suka baci da yadda za’a gyara. Tundaga kan masu yin dokoki da masu zartarwa da hukumar shari’a da manyan ma’aikatan gwamnati. Yadda za’a tabbatarda tsaron rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini na kowa da kowa, ‘yan kasa da baki mazauna kasar da masu shigowa cikin kasar.
Sabanin irin halinda muke ciki a yanzu, aka sami shugabannin kasa barayi, shugabannin ‘yan sanda barayi, alkalin kotun koli da alkalin alkalai barayi. Hatta alkalan kotuna na musulunci barayin kudin marayu, ministocin shari’a barayi. A irin wannan hali su waye zasu kama masu kowanne irin laifi balle sata? Su waye zasu hukuntasu? Ko a lokacin jahiliyya ba haka suka rayu ba.
Mu faro daga jamhuriyya ta farko, duk Firimoyin kowanne bangaren Najeriya bamu ji wanda akayiwa tereren yayi sata ba, musamman namu na Arewa, jihohi goma sha tara da Abuja a yanzu, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto da Prime Minister, Sir, Abubakar Tafawa Balewa wadanda sojoji suka kashesu, babu wanda ya mallaki gida fiyeda daya ko kudi fiyeda fam dari daya (£100), babu wanda ya mallaki rijiyar mai ko gidan mai ko motar dakon mai, babu wanda ya azurta iyalansa ko ‘ya’yansa ko ‘yan uwansa ko surikansa ko abokansa ko ministan mai da lantarki balle wasu jakunan barayi ko hannayen jari a wasu kamfanoni ko masana’antu, gida da waje.
Yaya abin yake a yanzu? Kusan kowanne mai mulki babba da karami barawo, dan’ kungiyar asiri ko Cabal. Sun mallaki rijiyoyin mai da bankuna da rukunin gidaje da kamfanoni da masana’antu.
Ina wadanda aka zalunta; manoma da makiyaya da masu sana’o’in hannu da masu hakar ma’adanai da marasa aikinyi da wadanda rushewar darajar naira da bankuna suka rutsa dasu da wadanda aka dannewa hakki, aka ci zarafin su, akayiwa fyade, akayiwa kisa ko sata? Ina ‘yan siyasa irin na da? Ina ‘yan kasuwa irin na da? Ina malaman addini irin na da? Ga aikin Allah ya samemu. Idan gurguzu da jari hujja sun gaza sai kuma me? Idan malaman addini sun gaza ina dalibai? Afghanistan ta ishi duk masu hankali abin koyi. ‘Dalibai (Taliban) sun kawarda mulkin zalunci da fajirci da sata da kisa.
Duk wanda yace wani canji ba zai yiwu ba, shine ba ya so a canja! Allah shine kadai idan ya ce wani abu ba zai yiwu ba, babu wanda ya isa ya yi! Allah shine ya halicci kowa da komai, gareshi duk zamu koma, ba ga Yahudu ko Nasara ko ‘yan kungiyar asiri da Cabal ba. Ba ga ‘yan bokon kauye da wawayen birni da bokaye da matsafaba.
Ina kira ga daliban addini da na kasuwanci na halal da daliban siyasa masu burin samarda canji na alkhairi wanda kowa da kowa zai sami hakkinsa, kowa ya girbi abinda ya shuka, ayiwa kowa adalci, suzo mu hadu mufara darasin siyasa ta neman ‘yanci da hakki tun daga matakin farko.
Alhamdulillah, nidai na shirya. Allah ya hada kawunanmu, ya shige mana gaba, ya yi mana jagora, muyi nasara, mugama da duniya lafiya, mu cika da imani! Ameen, thumma ameen!
Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, Tsohon Shugaban AD na Kasa, Tsohon Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Aiyukan Noma ta Jihar Kano.
08023106666, 08060116666, 09094744184.