For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Muhammad Abacha Ne Dan Takarar Gwamnan Kano A PDP – Kotu

Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano ta yanke hukuncin cewa Muhammad Abacha ne ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

BBC Hausa ta rawaito cewa, Alkali A. M Liman ne ya yanke hukuncin a yau Alhamis ta manhajar Zoom kasancewar ba ya gari.

Ya ce bangaren da suka gudanar da zaben fitar da gwani a Lugard Road shi ne halastaccen zaben dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP.

Tun bayan ficewar Rabi’u Musa Kwankwaso ne rikici ya ƙara ƙamari a jam’iyyar PDP ta Kano ta yadda har aka samu rarrabuwar kawuna a zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamna.

Ɓangaren Aminu Wali ya fitar da ɗan takararsa Sadiq Wali yayin da ɓangaren Shehu Sagagi ya fitar da Muhammad Abacha a matsayin nasa ɗan takarar.

A zaben fitar da gwani da aka yi a watan Mayun 2022, Mohammed Abacha ya fafata da Adamu Yunusa Ɗan Gwani da Ibrahim Al-Amin Little da Muhiyi Magaji Rimin Gado da Jafar Sani Bello da kuma Injiniya Mu’azu Magaji wato Ɗan Sarauniya.

Kuma a lokacin sakamakon ya nuna Muhammad din ne ya yi nasara.

Sai dai a watan Yuli kuma sai ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta wallafa sunan Sadiq Aminu-Wali a matsayin dan takarar PDP na jihar ta Kano.

Comments
Loading...