A daren Talata ne aka sami wani mummunan hari kan gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Harin wanda akai amfani da abubuwan fashewa da bindigu, ya bar mazaunan yankin cikin fargaba da tsoro.
A sanyin safiyar ranar Laraba, ba a sami tabbacin abun da ya faru ba, haka kuma, hukumomi da shaidun gani da ido na gudun cewa komai game da lamarin, abun da ya sa ‘yan Najeriya da dama jefa tambayoyi kan abun da ke faruwa.
A kokarin bibiya na abubuwan da suka biyo lamarin, CHANNELS TV ta waro wasu muhimman abubuwa bakwai yayin TASKAR YANCI ta kara da wasu abubuwa biyu da suka faru game da lamarin.
An Kashe Mutane Hudu
Da take jawabi kan lamarin, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ce, mutane biyar ne aka kashe a lokacin harin. Jami’in hukumar, Umar Abubakar, a ranar Laraba ya bayyana cewa, fursunoni uku ne suka rasa rayukansu a lokacin hayaniya, yayin da ‘yan bindiga suka kashe jami’in NSCDC guda daya.
Mutane 19 Ne Suka Ji Rauni
A game da mutanen da suka ji raunuka kuma, Abubakar ya ce fursunoni 16 ne suka sami raunuka, yayin da jami’an NSCDC 3 ma suka sami raunuka.
Ya bayyana cewa, dukkaninsu suna karbar magani.
Fursunoni Sama 800 Ne Suka Tsere
Umar Abubakar ya bayyana cewa, fursunonin da basu gaza 800 ba ne suka tsere a yayin harin.
Ya ce, fursunoni 879 suka tsere daga gidan yarin, inda ya kara da cewa “an kamo fursunoni 443 yayin da a yanzu haka ake da fursunoni 551 a gidan yarin, sai kuma 443 wadanda har yanzu suna waje,” sai dai kuma wannan adadi bai bayar da lissafin dai-dai ba duban da cewa, akwai fursunoni 994 a gidan yarin kafin a kawo harin.
Dukkan ‘Yan Boko Haram 64 Da Ke Gidan Yarin Sun Tsere
Biyo bayan nazarinsa game da harin, Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya bayyana cewa, dukkanin ‘yan Boko Haram 64 da ake tsare da su a gidan yarin sun tsere.
DCP Abba Kyari Da Sauran Manyan Mutanen Da Ke Gidan Suna Nan Kalau
Sabanin rahotannin da ke zagayawa cewa, DCP Abba Kyari ya tsere a lokacin harin, Hukumar Kula da Gidajen Yarin ta ce, dansandan da sauran manyan mutanen da ke tsare a gidan suna nan karkashin kulawar gidan yarin.
An Yi Amfani Da Abubuwan Fashewa A Harin
A jawabinta, Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Kasa ta bayyana cewa, maharan sun yi amfani da abubuwan fashewa wajen fasa babbar kofar shiga gidan yarin na Kuje da kuma ruguza katangar gidan, inda a wannan ne jami’in NSCDC ya rasa ransa.
An Yi Zargin ‘Yan Boko Haram Ne Suka Kitsa Harin
Bayan kai harin, duba da adadin ‘yan Boko Haram da suka tsere a yayin harin, Ministan Tsaro, Bashir Magashi ya ce, akwai kakkarfar alamar da ke nuni da cewa ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram ne suka kai harin.
Kungiyar ISWAP Ta Dauki Alhakin Kai Harin
Kungiyar ISWAP da ke a matsayin wani yanki na kungiyar Boko Haram da ya balle, sun bayyana cewa sune suka kai hari kan gidan yarin Kuje a wani faifan bidiyo da ta saki a jiya Laraba da daddare.
Faifan bidiyon ya nuna ‘yan ta’addar da dama yayin da suke ficewa daga gidan yarin suna kabbara.
Shugaba Buhari Ya Ce Tsarin Tsaron Najeriya Ya Ba Shi Kunya
Shugaban Kasa Muhammadun Buhari ya ce tsarin tsaron Najeriya ya ba shi kunya, inda ya ce, “Ta yaya ‘yan ta’adda zasu shirya, su sami makamai, su kai hari kan jami’an tsaro kuma su tsira?”.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar gidan yarin na Kuje a jiya Laraba, lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa Dakar na kasar Senegal wani taron kasashen Afirka.