For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mun Cafke Jirgi Marar Matuki Da Bamabamai Na IPOB A Iyakar Imo Da Anambra – Jami’an Tsaro

Jami’an Tsaron Najeriya sun kama jirgi marar matuki drone wanda suka ce Kungiyar ‘Yan Awaren Biafra, IPOB ne ta shigo da shi kasar daga wata kasa a yankin Asia domin aiyukan leken asiri.

Jaridar VANGUARD ta gano cewa, drone din wanda ana anfani da shi, an kirkire shi tare da shigo da shi ne a matsayin na’urar anfanin manoman yankin.

Bayan kwakkwaran bincike da leken asiri, jami’an tsaro sun kwace drone din daga wajen IPOB a Karamar Hukumar Orsu da ke Jihar Imo.

Rahotanni sun nuna cewa, baya da jirgin drone din, jami’an tsaron sun kuma kwace bamabamai 225 da sauran kayan fashewa a wannan waje da ke iyakar Jihar Imo da Jihar Anambra.

A ranar Alhamis da ta gabata ma, jami’an ‘yansanda sun kwato makamai masu hatsari daga ‘yan kungiyar ta IPOB a Jihar Ebonyi.

Comments
Loading...