Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta rage tsadar kuɗin karatu maimakon samar da tsarin bashi ga ɗalibai.
Shugaban Ƙungiyar, Henry Okuomo ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a, a wata hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na Channels Television.
Okuomo ya ce zai fi amfani ga ɗaliban Najeriya idan aka rage kudin rijistar karatu maimakon basussuka da za su iya gagarar biya saboda rashin ayyukan yi da ake fama da shi a ƙasar.
Ya ƙara da cewa, maimakon basussuka, gwamnati ta rage kuɗaɗen karatun da ake biya a manyan makarantu zuwa tsakanin N20,000 da N50,000, domin hakan zai bai wa kowa damar samun ilimi idan kuɗin rijistar ya sauƙa.
Ya bayyana cewa, duk da tsarin bashin da gwamnati ta samar, har yanzu ba su san yanda za a biya bashin ba kuma ba su san waɗanda suka ci gajiyarsa ba.
Okuomo ya ƙara da cewa, akwai ɗaliban da suka nemi bashin amma ba su samu ba, duk da ƙoƙarin da suka yi wajen neman.
Ya bayyana cewa sun tuntubi hukumar NELFUND game da batun, amma har yanzu ba su samu amsa daga gare ta ba.
A baya dai TASKAR YANCI ta rawaito cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bayar da bashi ga ɗalibai a ranar Laraba, 3 ga Afrilu, bayan amincewar Majalisar Dattawa a ranar 20 ga Maris, 2024, duk da cewar ASUU ta yi Allah wadai da dokar.