Kungiyar Dattawan Arewa ta ce ta yi nadamar nuna goyon baya ga Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015, a madadin Goodluck Jonathan.
Kungiyar ta kara da cewa Buhari ya yi watsi da mafi yawan ‘yan Najeriya da sukai kwadayin shugabancinsa kafin zaben 2015.
A cewar Daraktan Yada Labarai da Wayar da Kai na kungiyar, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, kungiyar ta su na son shugaban Najeriya na gaba ya zama wanda zai yi aiki ba irin na shugaban Najeriya mai ci yanzu ba.
Daraktan ya yi wannan magana ne lokacin da ake hira da shi a shirin safe ‘The Morning Show’ na gidan talabijin na Arise TV.
Baba-Ahmed ya ce: “Shin akwai wani dan Najeriya da bai ji takaicin yanda Shugaba Buhari yake Mulki ba, har da ‘yan APC? Shin akwai wanda ba zai ce maka ya yi fatan shugaba Buhari ya yi abin da yafi haka ba?
“Mun sa rai da yawa, mun gaya wa mutane, ‘Ku kawar da Jonathan, ku kawo Buhari, zai magance cin hanci da rashawa, zai gyara matsalar tsaro, zai gyara tattalin arziki (amma) ku duba inda muke yanzu.
“Ta yaya wani zai ce yana farin ciki da tarihin Shugaba Buhari a wannan? hatta mutanen da ke kusa da shi za su gaya muku cewa sun yi fatan zai iya yin abubuwa da yawa kuma zai iya yin abin da ya fi haka amma ga shi bai yi ba.
“Don haka, abin da muke bukatar yi yanzu shi ne mu shirya don zaben wani shugaban, wanda zai zama sabanin haka, shugaban da ke da hangen nesa da kuma kyakkyawan tunanin abin da mulki ya kunsa ba zama shugaban ba kawai.
“Don haka, na yi takaici kuma shi ya sa a yau, na himmatu sosai wajen kokarin ganin cewa sabon shugaba ya bullo da sabon salon rayuwa ga ‘yan Najeriya, “in ji Baba-Ahmed.
In za a iya tunawa, Kungiyar Dattawan Arewa a zaben 2015, ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Buhari, sai a watan Disamba na 2020 ta canza in da ma ta nemi shugaban da ya ajiye aikinsa saboda ba zai iya ba.
Sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir Ya Rasu
Allah Ya yi wa Sarkin Gaya a jihar Kano Alhaji Ibrahim Abdulkadir rasuwa a yau Laraba.
Mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook.
Acewar sanarwar da sakataren gwamnatin jihar ya fitar nan gaba kadan za ta fitar da sanarwar a hukumance.
Sarki Ibrahim Abdulkadir ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
Sarkin ya rasu yana da shekara 91, kuma ya shafe shekaru 30 yana mulkin Gaya wanda a daga baya ya zama Sarki a shekarar 2020.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya mayar da Sarkin Gaya Sarki mai daraja ta daya, tare da sauran masaratu uku a jihar Kano.