For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Gwamnatinmu Ta Fifita Samar Da Ababen More Rayuwa – Shugaba Buhari

Daga: Kabiru Zubairu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya gudanar da taron tattaunawa tsakanin kasashe biyu a cigaba da taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York na Amurka, tare da Mai Martaba, Maxima Zorreguieta, Sarauniyar Netherlands, a lokacin da ya ce Najeriya na sane da iyakokin ta, don haka ya ba da fifikon samar da ababen more rayuwa.

“Idan babu ababen more rayuwa, ci gaba zai takaita, saboda haka muna mai da hankali kan gina hanyoyi, layin dogo, da samar da wutar lantarki.

Muna da cikakken tsari, kuma muna iyakar kokarin mu,” in ji Shugaban.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa Sarauniyar, wacce ta taba ziyartar Najeriya a shekarar 2017, cewa idan ta sake zuwa, za ta ga bambance -bambancen da yawa.

Mai temakawa shugaban kan yada labarai da kafafan yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Femi Adesina ya ce, shugaba Buhari a bunkasa fannin aikin gona, ya ce “an rufe kan iyakokin Najeriya da kasashe makwabta don karfafa wa manoma gwiwa, da cin abin da muke nomawa”.

Mutane sun koma koma gona, kuma wannan ya taimaka mana kwarai.

Mun samar da takin zamani, mun kuma farfado da madatsun ruwa, wanda hakan sun yi tasiri mai kyau.

Badon haka ba, da kusan mutane miliyan 200 da muke a kasar, da mun kasance cikin matsala lokacin da COVID-19 ta shigo mana ta taba tattalin arzikin.”

Ya ce Najeriya za ta kara samun cigaba idan aka samu sanya hannun jari musamman a harkar noma.

Shugaba Buhari ya ce, “Muna da kasa, muna da mutane, sanya jari shine abin da muke bukata,”

Sarauniya Zorreguieta ta yaba da abin da ta kira “babban kokari” da Najeriya ta yi don yakar cutar Coronavirus, tana mai cewa; “Kun kashe babban manyan kudadenku a kai.”

Ta ce tana da babban alkawari ga Najeriya, “kuma za ta so ta goya mata baya ta don cimma abubuwa da yawa.

Ba za ku kasance ku kadai ba. Za mu kasance tare da sauran abokan huldarmu.”

Sarauniyar ta ce babban fatanta shine Najeriya ta samar da ababen more rayuwa, ta yadda masu saka jari da masu ba da agaji za su iya shiga yankunan da ba manyan birane ba.

“Muna bukatar hanyoyi, hanyoyin jirgin kasa, hada-hadar kudi na dijital ga manoma. Dole ne gwamnati ta sanya ido kan duk hadadar kudi,” in ji ta.

Comments
Loading...