For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Muna Iya Bakin Ƙoƙarinmu Wajen Ganin INEC Ta Yi Zaɓe Mai Inganci – Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa na yin iya bakin ƙoƙarinta ba tare da gajiyawa ba, wajen ganin an tabbatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta samu zarafin gudanar da ingantacce kuma sahihin zaɓe tare da miƙa mulki ga sabuwar zaɓaɓɓiyar gwamnati cikin nasara a shekarar 2023.

Shugaban Ƙasar ya fadi hakan ne jiya Alhamis a wani zama da yai da ƴan Najeriya mazauna Spain, a matsayin wani ɓangare na ziyarar aiki da yake yi a ƙasar.

Ƴan Najeriya mazauna ƙasar da suka halarci zaman sun haɗa da Shugaban Ƙungiyar Ƴan Najeriya Mazauna Spain, John Bosco; Mataimakinsa, Richard Omoregbe; ɗan wasan Ƙungiyar Super Eagles mai buga wasa a ƙasar, Kenneth Omeruo; jami’in hakokin ƙwallon ƙafa, Obinna Okafor; ɗalibi mai karantar harkokin tuƙin jiragen sama, Mohammed Bashir; ɗalibi mai karantar harkokin duniya, Segun Adedoyin; da kuma wani ɗan kasuwa, Bright Omorodion.

Ganawar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Ƴan Najeriya Mazauna Spain

A jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya raba, Buhari ya ce, Najeriya ta riga ta tsunduma cikin shirye-shiryen da zasu kai ta ga gudanar da zaɓen shekarar 2023.

Shugaba Buharin ya ƙara da cewa, “An yi haka ne domin ƙarfafa demokradiyyarmu kuma domin mu zama ababan koyi ga sauran ƙasashen Afrika”.

Shugaban Ƙasar wanda yai alƙawarin cewa, Najeriya zata ci gaba kare muradan ƴaƴanta mazauna ƙasashen waje, ya kwatanta ƴan Najeriyar mazauna Ƙasar Spain a matsayin wakilai na gari.

Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau Juma’a bayan kammala ziyarar aiki da ya kai ƙasar ta Spain.

Comments
Loading...