For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mutane 3 Sun Mutu, An Kubutar Da 18 A Karshen Binciken Ginin Da Ya Rushe A Delta

An tabbatar da mutuwar mutane uku bayan rushewar ginin coci a Okpanam da ke jihar Delta.

Wata mata da wasu yara mata biyu ne suka ransu a hatsarin da ya faru a ranar Talata a karamar hukumar Oshimili ta Arewa da ke jihar.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yansandan jihar Delta, Bright Edafe ne ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu, inda ya kara da cewa mutane 18 da ginin ya rufe su an samu damar ceto su.

KU KARANTA: Kaso 4.2 Cikin 100 Kawai Aka Gama Yiwa Rigakafin Korona A Najeriya

Har yanzu dai babu tabbacin cewa, wadanda aka ceto din duk yara ne, amma dai rudunar ta sanar da cewa an kammala aikin ceton.

Jami’in ya kuma ce, 15 daga cikin wadanda aka ceto sun samu raunuka, yayin da aka sallami 4 daga cikinsu daga asibiti, inda 11 kuma ke karbar magani har yanzu.

Wata majiya, ta jiyo cewa Mataimakin Gwamnan jihar, Kingsley Otuaro zai ziyarci inda hatsarin ya faru.

Akwai yiwuwar zai amsa wasu daga cikin tambayoyin da suka shafi dalilin faruwar hatsarin da kuma matakin da gwamnati za ta dauka domin kare faruwar hakan a nan gaba.

Hatsarin na faruwa, jami’an agaji na red cross da masu kashe gobara da kuma jami’an tsaro suka isa wajen domin aikin ceto.

Comments
Loading...