For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mutane 31 Ne Suka Mutu Saboda Turmutsitsin Taro A Jihar Rivers

A kalla mutane 31 ne suka mutu a turmutsitsi a yayin taron gangamin da wata coci ta shirya a birnin Fatakwal na jihar Ribas, da safiyar ranar Asabar, kamar yadda hukumar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana.

Grace Iringe-Koko, kakakin hukumar ‘yan sandan jahar, ta tabbatarwa ‘yan jaridu hasarar rayukan da ya faru a wajen taron gangamin na Fatakwal, ta ce lamarin dai ya faru ne yayin da wani coci a babban birnin jihar ya shirya bayar da tallafi ga masu karamin karfi a cikin al’umma, inda a yayin kaddamar da shirin ne aka samu faruwar wannan mummunan al’amari.

A cewar kakakin ‘yan sandan, da farko an tsara gudanar da rabon tallafin ne da misalin karfe 9 na safe agogon wurin, amma saboda da wasu mutane sun riga sun isa wajen tun da wurwuri, kana suka kutsa zuwa wajen, lamarin da ya haifar da turmutsitsi.

Da take bayani ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, Iringe-Koko ta ce, jami’an ayyukan ceto na gudanar da aiki a wajen da lamarin ya faru, kana tuni ‘yan sanda sun kaddamar da fara bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.

Daga: CRI HAUSA

Comments
Loading...