A kalla mutane 5 ne suka mutu, mutane 19 kuma suka ji rauni lokacin da wata kakkarfar girgizar kasa ta girgiza kudancin kasar Iran a safiyar yau Asabar.
Girgizar kasar mai karfin 6.0 ta shafi waje mai fadin kilomita 100 (mil 60) na Kudu maso Yammacin birnin Bandar Abbas a yankin Hormozgan, in ji rahoton bincike da United States Geological Survey ya fitar.
IRNA ta rawaito Gwamnan Hormozgan, Mahdi Dosti na cewa, girgizar kasar ta kashe mutum 5 tare da jikkata mutane 19.
Gwamna Dosti ya kuma kara da cewa, mafi yawan ta’adin da girgizar kasar ta yi, ya faru ne a kauyen Sayeh Khost.
A watan Nuwambar bara ma, mutum daya ya mutu a yankin Hormozgan lokacin da tagwayen girgizar kasa suka faru masu karfin 6.4 da kuma 6.3.
Ana yawan samun girgizar kasa a kasar Iran, kuma wadda ta fi karfi a tarihi ita ce wadda ta faru a shekarar 1990 mai karfin 7.4 inda tai sanadiyyar mutuwar mutane 40,000 a arewacin kasar.
AFP