For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mutane Rabin Miliyan Ne Suka Rasa Gidajensu Yayin Da Mutane 30 Suka Mutu A Ambaliyar Ruwan Borno

Aƙalla mutane 414,000 ne suka rasa matsugunansu yayin da wasu 30 suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a ranar Talatar da ta gabata.

Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa ambaliyar ta faru ne bayan cikar Alau Dam da ruwan sama mai yawa, wanda ya haddasa ambaliyar mafi muni cikin shekaru 30 a garin.

Mai Magana da Yawun NEMA, Manzo Ezekiel, ya shaida wa jaridar PUNCH cewa mutanen da suka rasa rayukansu sun kai 30, yayin da fiye da rabin miliyan suka rasa gidajensu.

NEMA ta ƙara da cewa ambaliyar ta shafi gidaje sama 23,000, bayan da madatsar ruwa ta Alau dake tafkin Ngadda mai tazarar kilomita 20 daga Maiduguri ta ɓalle.

Bayanan NEMA sun nuna cewa ambaliyar ta mamaye kaso 70 cikin 100 na garin, ciki har da fadar Shehun Borno, Umar Ibn Garbai El-Kanemi, ofishin gwamnati, gidan waya, asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri da maƙabartar garin.

Ambaliyar ta kuma kashe dabbobi 80 cikin 100 na gidan namun daji na Sanda Kyarimi, ta lalata gidaje, makarantu, wuraren kasuwanci da kuma wuraren ibada.

Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwarsa kan ambaliyar, inda ya umurci hukumomin gwamnati da su hanzarta aikin ceton mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya bayyana cewa fiye da mutum miliyan ɗaya ne ambaliyar ta shafa, inda Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan uku domin tallafa musu.

Gwamna Zulum ya rarraba kuɗaɗe da abinci ga dubban mutanen da suka rasa gidajensu, inda aka fara ba da N10,000 ga kowanne gida don rage raɗaɗin asarar.

Wasu daga cikin fursunonin gidan yarin Maiduguri sun tsere sakamakon lalacewar katangar gidan, amma an kama uku daga cikin waɗanda suka tsere.

Alkaluma sun nuna cewa ruwan ambaliyar ya ragu a yankuna kamar Modugari, Kofar Shehu, da Ofishin Gidan Waya, kamar yanda wani mazaunin garin ya tabbatar.

Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa suna ci gaba da aikin ceto, tare da tattara bayanai game da waɗanda ambaliyar ta shafa, don tallafa musu.

Comments
Loading...