Mutanen da ba su gaza 9 ba ne suka rasa rayukansu sannan da dama suka ji raunuka a wani rikicin makiyaya da manoma da ya faru a Ƙaramar Hukumar Guri da ke jihar Jigawa.
Jaridar THE NATION ta rawaito cewa, rikicin ya fara ne tun a makon jiya bayan wani makiyayi ya yi gangancin kashe wani manomi a garin Guri tare da lalata gonar shinkafarsa.
Wata majiya daga garin ta fadawa wakilin THE NATION ta wayar salula cewa, makiyaya 6 da manoma uku ne suka mutu a dalilin rikicin.
“Wani makiyayi ne ya kai hari wa wani matashi a gona, ya kuma kashe shi,” in ji majiyar.
“Lokacin da manoma a garin suka gano lamarin, sai suka kai harin ramuwa kan Fulani.”
Jami’in yaɗa labarai na Ƙaramar Hukumar Guri, Malam Sunusi Alhaji Doro ya ce, an rufe dukkanin makarantun da ke yankin har sai baba ta gani saboda rikicin.
“An rufe makarantun Nomadic saboda mafi yawan malaman makarantun mutane ne da suka fito daga ɓangaren manoma, waɗanda suka dena zuwa wajen aiki saboda tsoron kar a kai musu hari.”
Alhaji Doro ya ƙara da cewa suma Fulanin sun dakatar da zuwa kasuwanni da kuma garin na Guri, yayin da manoma suka dena fita gonakinsu.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Jigawa, Lawal Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai kuma ya ce mutum biyu kaɗai aka kashe a rikicin.
“An samu rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Ƙaramar Hukumar Guri, inda mutane biyu suka rasa rayukansu, mutane biyar kuma suka ji raunuka.”
Shiisu ya ƙara da cewa, Kwamishinan Ƴansanda na Jihar Jigawa, Sale Aliyu Tafida ya kai ziyara wajen da abin ya faru.
Ya kuma ce, an kama waɗanda ake zargi da hannu a rikicin su 10.
(THE NATION)