For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mutum Biyar Sun Ji Raunuka, Gine-Gine 22 Sun Lalace Sanadiyyar Fashewar Gas A Jigawa – NSCDC

Rundunar Jami’an Tsaro ta Civil Defence a Jihar Jigawa, ta yi karin haske kan fashewar gas da ya faru jiya a Karamar Hukumar Babura da ke jihar, inda ta ce mutane biyar ne suka sami raunuka a dalilin fashewar.

Mai Magana da Yawun rundunar, Adamu Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata ya ce, shaguna 17 da gidaje 5 ne suka kone a sanadiyyar wutar da ta tashi dalilin fashewar.

Ya kara da cewa, lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin da misalin karfe 9, bayan jami’an tsaro da ke binciken ababan hawa a kan iyakar Najeriya da Nijer sun gano motar daukar kaya mai dauke da tunkunyar gas 25.

Ya kuma yi zargin cewa, direban motar ya ki ya tsaya bayan jami’an sun biyo shi, abun da ya jawo daya daga cikin tunkunyar gas ta fado ta kama da wuta nan take.

Adamu Shehu ya kuma ce, motar ta taho ne daga garin Tinkim da ke Karamar Hukumar Magarya a Jamhuriyar Nijar kuma tana kan hanyarta ta zuwa Karamar Hukumar Hadejia ne lokacin da lamarin ya faru.

Ya kuma ce, wadanda hatsarin ya rutsa da su, yanzu haka suna karbar magani a Babban Asibitin Babura.

Comments
Loading...