For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mutum Daya Ya Mutu, Uku Sun Ji Rauni A Harin Gidan Yarin Kuje

Akalla mutum daya ne ya mutu, yayin da mutane uku suka ji raunuka a harin da aka kai Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke babban birnin tarayya, Abuja.

A jiya Talata ne da yamma, aka ji karar tashin abubuwan fashewa da bindigu a gidan yarin, abun da ya jawo rashin nutsuwa ga mazauna yankin na Kuje.

Kasa da awanni 24 da faruwar lamarin, Gwamnatin Tarayya ta ce, wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun balla gidan yarin domin su kubutar da mambobinsu.

Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Al’amuran Cikin Gida, Shuaibu Belgore ne ya bayyana hakan a yau Laraba, lokacin da ya kai ziyara gidan yarin.

Ya bayyana cewa, sama da ‘yan fursuna 300 ne aka samu dawowa da su, sannan kuma ana kokarin dawo da sauran.

Ya kara da cewa, ‘yan fursuna 600 ne suka tsere daga gidan yarin a yayin harin jiya da daddare.

Duk da har kawo wannan lokaci rundunar ‘yansanda ba su saki sanarwa kan lamarin ba, mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali, AD Umar ya ce, an samu nutsuwa game da lamarin bayan shigar jami’an tsaro ciki.

“Ina farincikin tabbatar da cewa, da misalin karfe 10 na dare, wadansu ‘yan bindiga da har yanzu ba a tantance ba sun kai hari Cibiyar Ajjiya mai Matsakaicin Tsaro (da ke) Kuje a Babban Birnin Tarayya,” in ji Umar.

“Haka kuma, jami’an tsaro masu rike da makamai na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali da sauran jami’an tsaro daga wasu hukumomin da ke aiki da Cibiyar Ajjiyar sun mayar da martani kuma an samu nutsuwa yanzu komai ya dawo dai-dai.”

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ‘yan bindiga ke kai hari kan gidajen yari ba a kasar, su saki fursunoni bayan sun kashe wasu daga cikin masu tsaron gidajen.

A lokacin harin da aka kai gidan yarin Owerri da ke Jihar Imo ranar 4 ga Afrilun shekarar 2021, ‘yan bindigar sun kubutar da fursunoni 1,844 bayan sun yi amfani da abubuwan fashewa wajen fasa gidan yarin.

Comments
Loading...