For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mutum Dubu 20 Sun Isa Ukraine Don Taimaka Mata A Yaki Da Rasha

Gwamnatin Ukraine ta ce akalla ‘yan kasashen waje 20,000 suka isa kasar domin taimaka mata yaki da sojojin Rasha dake neman karbe iko da kasar baki daya.

Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya tabbatar da haka, inda yake cewa bakin sun fito ne daga kasashen Turai da dama.

Kuleba ya bayyana mutane da dama a matsayin masu kyamar Rasha saboda matakan da take dauka a yan shekarun nan, amma kuma babu wanda zai iya adawa da ita ko kalubalantar ta.

Ministan ya ce ganin yadda Yan kasar Ukraine suka tashi domin kare kasar su, matakin ya baiwa jama’a da dama kwarin gwuiwar shiga yakin domin hukunta Rasha akan matakan da take dauka na mamaya.

Kuleba ya ce yayin da wadannan mutane ke taimaka musu, suna bukatar jagorancin Amurka wajen samun taimakon soji daga sassan duniya da kuma jagoranci.

A makon jiya, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gayayci ‘yan kasashen wajen da suje domin taimakawa kasar yaki da Rasha bayan ta kaddamar da shirin mamayar.

Wannan kira ya sa Sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Liz Truss baiwa yan kasar izinin tafiya Ukraine, amma kuma ayau lahadi Babban Hafsan sojin kasar Admiral Tony Radakin yace sabawa doka ne Yan Birtaniya sun shiga yakin da ake tsakanin Rasha da Ukraine.

(RFI HAUSA)

Comments
Loading...