Wani hatsarin taho mu gama a jihar Kano ya jawo mutuwar mutane 12 a dai-dai kauyen Tsamawa da ke yankin Karamar Hukumar Garun Malam.
Mai Magana da Yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi ya baiyana cewa hatsarin ya jawo kamawar wuta wadda ta kone motocin tare da mutanen da suke ciki gaba daya ta yanda ba a iya gane su.
Ya kara da cewa, motocin hayar guda biyu da suka hadu sun hada da motar hiace wadda ke dauke da fasinjoji 11 wadda kuma ta taho daga Zaria za ta Kano, da kuma mota kirar J5 da ta taho daga Kano za ta Kaduna.
Karfin wutar da ta kama motocin ta cinye komai ta yanda ba a iya gano lambobin motocin ba da kuma mutanen da ke ciki a lokacin hada wannan rahoton.
Saminu Yusif ya baiyana cewa, ana zargin rashin bibiyar ka’idojin bin hanya a matsayin abin da ya haddasa hatsarin.
Ya yi kira ga ‘yan uwan wadanda suka bi hanyar da su tuntubi Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano domin a gano wadanda sukai hatsari.
(RADIO NIGERIA)