Mutanen da ba su gaza 10 ba ne aka tabbatar sun mutu lokacin da gini mai hawa 21 ya zube a kan titin Gerard da ke Ikoyi a jihar Lagos.
A lokacin da ake shirya wannan rahoto, akwai sauran mutane da ke karkashin baraguzan ginin ciki har da Manajan Darakta na Fourscore Hights Limited, Femi Osibona, wanda shine mamallakin ginin, da kuma sauran abokan huldarsa da injiniyoyi.
Ginin dai ya rushe ranar Litinin da misalin karfe 2 na rana lokacin ma’aikata na tsaka da aiki.
Daya daga cikin ma’aikatan da suka tsira a hatsarin, Gabriel Bassey, ya sanar da wakilin PUNCH cewa akwai akalla mutum 50 wadanda har yanzu ke cikin baraguzan ginin da ya rushe.
Ya ce, “Wannan aiki, mai 360 digiri, kamfanin Fourscore Homes Limited ke gina shi. Na yi kokarin sa waya ta a caji, ban fi sakankuna biyar ba da barin wajen na ginin yana rusowa, inda nai gudu natsira. Muna da mutane da yawa da ginin ya danne wadanda muke bukatar mu fito da su.
“Lokacin da abun ya faru, mun fito da gawarwaki shida, kuma har yanzu muna da kusan birkiloli ‘yan kasar Togo da ‘yan Nigeria da suka kai 30 da kuma injiniyoyi guda hudu da sauran ma’aikata. Shugabana, Mista Femi, har yanzu yana cikin baraguzan. Lokacin da abun ya faru yana hawa na 18 tare da wasu abokan huldarsa wadanda suke son siyan ginin a lokacin da bun ya faru.
Wani mazaunin yankin da abin ya faru, Morris Ashiobi, ya ce ginin bai nuna wata alama da faduwa ba, kawai dai gani akai ya zube.
Ya ce, “Lokacin da hatsarin ya faru, nine na farko da ya hau kan barguzan ginin har zuwa hawa na karshe, inda na gawarwaki. Na fara kiran mutane don su zo su ceci mutane. Mun gano gawarwaki shida, mun ceci mutum daya inda saura kuma har yanzu suna cikin baraguzan.
“Ginin bai nuna wata alama ba, kawai rushewa yai. Muna cikin aiki akansa. An debi awa guda kafin masu bayar da tallafin gaggawa su iso wajen kuma mun fito da gawarwakin mun kuma ceci mutum daya kafin su zo. Idan ba kuskure nai ba, ina tunanin akwai mutane kusan 40 a wajen, saboda lokacin muna tsaka da aiki. Wasu mutanen sun zo daga Abuja yau (Litinin) domin yin aiki. Ina da abokai da dama da har yanzu suna karkashin baraguzan ginin.
“Lokacin da ‘yan sanda suka zo, sun kore mu daga wajen ba su bar mu mun cigaba da ceton mutane ba, da sun bar mu da mun kara ceton wasu.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Lagos, Hakeem Odumosu, ya tabbatar da mutuwar mutane biyar dalilin hatsarin, inda ya kara da cewa an ceci wasu mutane guda 3.
Haka kuma, Ko’odinata na Kudu maso Yamma na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, Ibrahim Farinloye, ya ce an gano gawarwaki hudu an kuma ceci mutane hudu daga ginin.
Wakilan PUNCH sun bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan uwan wadanda ginin ya zubowa na nan a wajen da abin ya faru suna ta rafka kuka kuma sun ki su yiwa manema labarai magana.