For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mutuwar Mutane Sanadiyyar Ayyukan Ta’addanci Ta Karu A Nahiyar Afrika

Sakatare Janar na Majalissar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce, yayin da adadin wadanda ke mutuwa sanadiyyar ayyukan ta’addanci ke raguwa a sassan duniya, adadin na karuwa ne a nahiyar Afrika.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne jiya, yayin taron yarjejeniyar hadin gwiwa kan yaki da ta’ddanci a duniya na Majalissar Dinkin Duniya.

A cewarsa, kungiyoyin ta’addanci kamar al-Qaida da IS da rassansu na ci gaba da karuwa a yankin Sahel, tare da kutsawa yankin tsakiya da kudancin nahiyar Afrika.

Ya ce biyo bayan ziyararsa a Jihar Borno dake arewacin Najeriya da ta kasance tungar kungiyar Boko Haram, yana da yakinin cewa, ana kan hanyar cimma sulhu tare da kara shigar da tubabbun ’yan ta’adda cikin al’umma.

Ya kara da cewa, shirin gwamnatin Najeriya shi ne, karfafa aminci tsakanin al’umma da kuma rushe tsarin kungiyar Boko Haram na horar da mayaka.

Yana mai cewa, yanzu haka, mayakan Boko Haram da suka tuba na komawa cikin al’umma, kuma jama’a ne da kansu, suka raunata ayyukan Boko Haram.

A cewarsa, ingantacciyar dabara na da muhimmanci ga tsarin yaki da ta’addanci na Majalissar Dinkin Duniya, yana mai kira da kara mayar da hankali ga bangarorin kiwon lafiya da samar da ilimi da kariya da tabbatar da daidaiton jinsi da tsarin shari’a ga kowa da samar da tsarukan demokaradiyya, ta yadda kowanne mutum zai iya bada gudummawa a cikin al’ummarsa da kasa baki daya.

(CRI HAUSA)

Comments
Loading...