Alamu na tabbatar da gaskiyar maganar karyata sakin sabbin ‘yan N-Power wadanda ake kira da Batch C Stream 2.
Kwanaki 3 da suka gabata ne aka samu sanarwar cewa an saki sunayen wadanda suka samu aikin N-Power a Batch C Stream 2.
Bayan samun sanarwar kuma, mutane da dama sun duba tare da yin dacen ganin sunayensu da bayanansu, abinda ya kai wadansunsu da yin thumbprint kuma duk yana yiwuwa.
To amma a sanarwar da shafin Twitter na N-Power @npower_ng ya saki a jiya Alhamis wadda kuma Ma’aikatar Jinkai da Walwala ta Minista Sadiya Umar Frouk ta sake wallafawa a shafinta na Twitter @FMHDSD an karyata wannan lamari.

Sanarwar ta gargadi mutane da su yi watsi da abin da ta kira da labaran kanzon kurege FAKE NEWS, inda ta ce hukumar kula da N-Power ba ta saki sunayen ‘yan N-Power Batch C Stream 2 ba har yanzu.
Sanarwar ta yi nuni da cewa akwai shirin sakin sunayen ‘yan N-Power Batch C Stream 2 amma ba a kai ga hakanba a yanzu.
Ta yi kira wajen bibiyar shafukffukan sa da zumunta na gaskiya wadanda suka shafi shirin N-Power domin samun sahihan bayanai.